1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

May ta tsallake kuri’ar yankar kauna

December 13, 2018

A yayin da aski ke kara matsowa gaban goshi dangane da ficewar Birtaniya daga Kungiyar Tarayyar Turai, alamu na nuni da cewar kasar ba ta san zuwa wane lokaci ne hakan zai tabbata ba.

https://p.dw.com/p/3A2y7
Brüssel Theresa May, Premierministerin Großbritannien
Hoto: Reuters/D. Martinez

A wannan  sharhin da Robert Turner na DW ya rubuta wanda ya yi wa take zuwa ga Birtaniya ya yi tambaya kai tsayye ga ‘yan Birtaniyar yana cewa Anya kuna da lokacin wannan kuwa? Kamar yadda lamura suke a yanzu, nan da 'yan makonni za ku fice daga Kungiyar Tarayyar Turai ba tare da cimma takamammiyar yarjejeniya ba. Kuma duk abun da wadanda ke goyon bayan wannan shiri na Brexit za su fada da ya sabawa hakan, zai zama babban hadari.

Sai dai idan har 'yan majalisar dokokinku suka zartar da doka a kan yarejeniyar ficewar, ko su dakatar da doka mai lamba  50, sabanin haka zaku fuskanci babbar matsala da shirin ficewa da EU.

Idan haka ne menene ya sa kuke bata lokacinku kan siyasar cikin gida? Idan da firaminista bata samu nasara a kuri'ar yankar kauna da aka kada ba, da zai daukeku tsawon makonni shida kafin ku samu sabon shugaban gwamnati. Bayan kuna da makonni 14 kacal kafin 29 ga watan Maris, wadda ita ce ranar zahiri ta barin EU.

Robert Turner na DW wanda ya wallafa sharhin
Robert Turner na DW wanda ya wallafa sharhin

Rana ta zahiri a kan Brexit

Irin kalaman da aka yi amfani da su ba kuskure ba ne. Ina kokarin magana da ku ne a cikin harshen da irinsa ne kadai wasunku za su fahimce ni." Birtaniya ta canja firaminista a watan Mayun 1940 a lokacin da kasar ke cikin rigingimun cikin gida da ya fi na yanzu. Idan har za'a yi abu to dole a yi shi kawai. Wadannan su ne kalaman da dan majalisar da ke goyon bayan ficewar Birtaniya da EU Bernard Jenkin ya wallafa a shafinsa na Tweeter bayan sakamakon kuri'ar yankar kauna kan Theresa May.

Tsuntsun da ya ja ruwa shi ruwa ke duka. Don me kuke neman juyawa shirin baya a yanzu? Don me kuke kara jefa kasarku cikin rudani da rarrabuwar kawuna? 

Yanzu wane zabi kuke da shi? Wani zaben kasa baki daya? Baku da lokaci? Wata kuri'ar raba gardama kan ficewa daga EU? Yarjejeniyar da ta hada Kanada da Norway da Switzerland da EU?

Akwai dai matsaloli da ke zube a kasa. Kuma Kungiyar Turai ta ce ya isa haka. Taronta na gaba a wannan Juma'arce, kuma babu wani karin lokaci na mahawara.

Aski dai na kara matsowa gaban goshi, sai dai kamar ba kwa ji. Watakila tsayar da sanannen agogon majalisar nan da ake kira Big Ben tun watan Afrilu domin gyara yazo akan gaba, aikin da zai dauki shekaru uku. Sai dai gyaran Birtaniyar zai dauki dogon lokaci fiye da haka.