1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Matakin EU kan Alexander Lukashenko

May 26, 2021

Shugabannin kasashen Turai suna aniyar taka birki ga takwaransu na Belarus Alexander Lukashenko kan matakin da ya dauka na tilasta wani jirgi sauka a kasarsa don kame wani dan adawa.

https://p.dw.com/p/3u0Ad
Belarus Minsk | Rede Alexander Lukashenko im parlament
Shugaba Alexander Lukashenko na BelarusHoto: Maxim Guchek/BELTA/AFP via Getty Images

Duk da wannan mataki na EU cikin wannan sharhin da ta rubuta, Barbara Wesel ta tashar DW na ganin da sauran rina a kaba. Ta ce matakin da shugabannin kasashen Turai suka dauka kan irin banga ko kuma jagaliyar siyasa da shugaban Belarus ke yi na da karfin gaske kuma abu ne da mai ratsa zuciya. Shugabannin sun kadu kana ransu ya baci da irin matakin shugaban na Belarus, wanda suka kira dan ta'adda da ke zaune a fadar shugaban kasa a Minsk babban birnin kasar. A wani yanayi na hadin kai da ba kasafai ake ganin irinsa ba, shugabannin na Turai sun dakatar da zirga-zirgar jirage zuwa kasar ta Belarus.

Karin Bayani: EU za ta dauki mataki a Belarus

Wannan mataki da suka dauka abu ne da zai yi tasiri sosai kan masu fada a ji a kasar, wanda galibinsu magoya bayan Lukashenko ne, matakin da a yanzu haka, ke kokarin mayar da Belarus saniyar ware a jerin kasashen duniya. Baya ga wannan mataki akwai kuma jerin takunkumai da za a kakaba wa kasar nan gaba kadan, wadanda za su shafi kamfanoni da daidaikun mutane. Kuma ga alama a wannan karon, shugaban na Belarus ba zai samu wanda zai goyi bayansa a wannan waki'ar da ta saukar masa ba, domin kuwa guda daga cikin wadanda ake ganin za su agaza masa wato shugaban Hungary Viktor Orban ma ya bi sahun takwarorinsa wajen mayar da Belarus din mujiya a cikin tsuntsaye.

Barbara Wesel Kommentarbild App *PROVISORISCH*
Barbara Wesel ta tashar DW

To sai dai duk da wadannan matakai da aka dauka na matsin lamba kan shugaban na Belarus, yana da kayau EU ta san irin hanyoyin da za ta bi wajen ganin sun tabbata, musamman ma idan aka yi la'akari da irin wadanda aka dauka a lokacin da Lukashenko ya yi ta kokarin murkushe masu zanga-zangar adawa da nasarar zaben da ya samu a watannin baya. A dangane da haka, ya kamata EU ta dau wasu karin matakai baya ga hana zirga-zirga da kuma sanya tankunkumi kan na hannun daman shugaban. Yanzu haka dai 'yan adawa a kasar na kiran da a haramta yin cikinkin danyan mai da kasar, wanda shi ne kan gaba wajen sama mata kudin shiga.

Karin Bayani: Har yanzu da sauran aiki gaba bayan taron Minsk

Ya kamata Turai ta gama kai da Amirka wajen tsaurara takunkumi na karya tattalin arziki ga kasar, domin sanya takunkumin ga daidaikun mutane da ke dasawa da shugaban abu ne mai wahala saboda irin tanadin da dokokin EU suka yi kan hakan. Irin yunkurin da shugaban dan kama-karya ya yi na tilasta jirgin sama ya sauka a Minsk tare da kame mai adawa da shi da ke ciki, ya kara tabbatar da irin abin da gwamnatin da ba ta karbuba tsakanin kasashen duniya za ta iya yi, duk kuwa da cewar karan Belarus bai kai tsaiko ba idan aka kwatanta da sauran kasashe.

Weltzeit 1 | 2021 | Protest-Ikone Nina Baginskaja, Belarus
Jami'an tsaro a Belarus, na kokarin murkushe masu zanga-zanga da 'yan adawaHoto: TUT.BY/AFP/ Getty Images

Wannan abu da shugaban na Belarus ya yi, zai iya sanya sauran shugabanni da ke da tunani irin nasa su  kwatanta hakan. Baya ga haka an ga irin yadda Chaina da Rasha ke karyawa inda ba gaba, idan wani abu ya hada su da abokan hamayyarsu, don haka dole a dau kwakkwaran mataki. Idan har kasashen duniya ba su dauki matakin ladabtarwa kan Alexander Lukashenko ba, to shakka babu mutane da yawa za su ci gaba da kasancewa cikin hadari na rasa rayukansu da kuma yin garkuwa da su don ko da gudun hijira mutum ya yi to fa ba lallai ya kasance ya tsira daga abin da ya gujewa ba.