Sharhi: Jamus ta canja | Siyasa | DW | 03.09.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Sharhi: Jamus ta canja

Jamusawa da yawa sun goyi bayan kalaman Merkel a bara cewa "Za mu iya" dangane da 'yan gudun hijira. Amma yanzu tana shan suka. Amma duk haka kasar na zama dandalin matsakaicin manufofin siyasa, inji Verica Spasovska.

Akwai wasu abubuwan da suka canja a Jamus tun bayan da shugabar gwamnati Angela Merkel ta furta wadannan kalaman a shekarar 2015. Da farko dai matsalar kyamar baki ta karu a Jamus. jam'iyyar masu ra'ayin rikau ta AfD wadda gabanin kwararowar 'yan gudun hijira ta rasa magoya baya, ta ci gajiyar fargabar da Jamus suka nuna a kan 'yan gudun hijirar. Kuri'ar jin ra'ayin jama'a ta baya bayan nan ta nuna jam'iyyar na da kashi 15 cikin 100 sabanin zaben 'yan majalisar dokoki na karshe inda ko kashi 5 cikin 100 ba ta samu ba balanta ta samu wakilici a majalisar dokokin tarayya.

Dandalin matsakaitan manufofin siyasa

Sai dai dole ne a kwatanta da sauran kasashen Turai, inda ga misali a kasashen Faransa da Bulgariya 'yan ra'ayin rikau na da wakilci a majalisun dokoki da fiye da kashi 20 cikin 100. A Hungary da Poland masu ra'ayin rikau suka kafa gwamnati. A Birtaniyya jam'iyyar kyamar baki ta UKIP ce ta haddasa mahawar janyewar kasar daga tarayyar Turai. Idan aka kwatanta da kasashen gabacin Turai masu matsanancin ra'ayyin kishin kasa, to har yanzu za a ga cewa Jamus na a matsayin wata kasa mai kwanciyar hankali da kuma matsakaitan manufofin siyasa.

Spasovska Verica Kommentarbild App

Verica Spasovska shugabar sashen Labaran intanet na DW

Ko da ya ke farin jinin shugabar gwamnati Angela Merkel ya ragu a tsakanin Jamusawa saboda rashin magance matsalar 'yan gudun hijira, amma matsayin jam'iyyarta bai wani canja sosai a tsakanin 'yan kasar ba. Ko da yake manufofinta dangane da 'yan gudun hijira ba su samu karbuwa a tsakanin da yawa na kasashen EU ba, amma tausayi da jin kai da ta nuna wa 'yan gudun hijira ya sha yabo ba ma daga shugaban Amirka Barack Obama kawai ba. Mutane da yawa daga Afirka da yankin Gabas ta Tsakiya sun daga mata tuta.

Fargabar ta'addanci ta karu

Ra'ayin Jamusawa game da 'yan gudun hijira ya canja. Bayan doki da haba-haba da aka nuna da farko, daga baya an an yi dari-dari. Cin zarafin matan da aka yi a jajiberen sabuwar shekara a birnin Kwalan da hare-hare masu nasaba da Musulunci da aka kai a garuruwan Ansbach da Würzburg sun sanya Jamusawa cikin fargabar fuskantar ayyukan tarzoma ta masu kaifin kishin addini, ko da yake maharan suna a Jamus lokaci mai tsawo gabanin bude iyakokin kasar a watan Satumban 2015.

Yanzu an gane cewa masu kishin Islama sun yi amfani tuttudowar 'yan gudun hijirar a bara sun shigo kasar. Sai dai da an rufe kan iyakoki da ba a iya taimaka wa daruruwa dubbai na mutane da ke neman taimako ba. Duk da wannan fargaba da rashin tabbas har yanzu ana ganin ragowar masu dokin bada taimakon a tsakanin Jamusawa.

Da jan aiki a gaba

Har yanzu da babban kalubale a gaban kasar. Dole al'ummomin da suka bada mafaka ga 'yan gudun hijira su zage dantse wajen sajewar bakin, wajen kai yara makaranta sannan magidanta a sama musu aikin yi. Duk wadannan na bukatar makudan kudade da kuma zai janyo mahawara da za ta iya yin illa ga kyakkyawar zamantakewar al'umma.

Ana bukatar nuna zumunci a kan batun na 'yan gudun hijira mai cike da kalubalai da kuma damarmaki a lokaci guda.

Sauti da bidiyo akan labarin