1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sharhi: Buhari na neman karin wa'adi

Moesch Thomas Kommentarbild App
Thomas Mösch
April 10, 2018

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya bayyana aniyarsa ta sake neman wani sabon wa'adin mulki a zaben gama-gari da za a yi cikin shekara mai kamawa. Hakan ya sa wasu sun ji dadi, yayin da wasu suka nuna damuwa.

https://p.dw.com/p/2vmTY
Nigeria Abuja -  Muhammadu Buhari nach Rückkehr aus England
Hoto: Reuters/Nigeria Presidency Handout

Nasarar da Buhari ya samu ta cin zaben shugaban kasa a shekaru ukun da suka gabata ta sanya galibin 'yan Najeriya kasancewa cikin farin ciki. Wannan lokacin shi ne karon farko da aka kayar da shugaba mai ci tun bayan da kasar ta samu 'yancinta daga hannun turawan mulkin mallaka a shekarar 1960. Bayan da ya lashe zabe Buhari ya yi alkwarin samar da tsaro da kawar da cin hanci da rashawa da kuma sanya bukatun mutane gaba fiye da komai.

 

Rayuwa ta yi tsauri a lokacin mulkin Buhari ba kamar yadda aka yi tsamanin samun sauki ba

Nigeria Boko Haram
Hoto: picture-alliance/AP Photo/J. Ola

To sai dai duk da wannan alkawura za ka ji ana fadin cewar rayuwa karkashin shugaba Buhari ta kasance mai tsauri fiye da yadda ta ke a baya. Idan ana batun tsaro kuwa, da fari an ga alamun nasara wajen fatattakar 'yan Boko Haram wanda suka mamaye wasu sassan kasar lokacin mulkin wanda ya gada na Goodluck Jonathan. Yakin da Buhari ya daura da 'yan  Boko Haram din ya sanya da dama daga cikinsu sun ranta a na kare inda suka koma cikin dazuka da tsaunuka sai dai daga baya sun koma cin karensu ba babbaka inda suka yi ta kai hare-hare. A baya-bayan nan ma abin ya kazanta.

Munin da matsalar tsaro ta yi a iya cewar ta bazu zuwa sauran sassan kasar ciki kuwa har da Taraba da Benue da ke tsakiyar kasar inda ake zub da jini kusa a kullum musamman ma tsakanin mabiya addinin Musulunci da na Kirista wanda manoma ne da kuma makiyaya. Kan wannan batu a iya cewar Buhari ya gaza warware matsalar kamar yadda Goodluck Jonathan ya gaza kawar da matsalar 'yan Boko Haram. To baya ga wannan ma dai, jihar Zamfara da ke makotaka da mahaifar Buhari ma dai na cikin tsaka mai wuya saboda gungun barayi na ta kashe-kashe ba tare da an iya yin maganinsu ba ko da dai a dan tsakanin nan Buharin ya girka wata rundunar soja da za ta yi aiki don tsaurara matakan tsaro a yankin.

 Cin hanci da karbar rashawa sun karu a karkashin mulkin gwamnatin na Buhari

Nigeria Plakate und Aufkleber gegen Korruption
Hoto: DW/K. Gänsler

Magance cin hanci wanda shi ne abu na biyu da ya sanya Buhari lashe zaben 2015 to amma abin da ke kasa shi ne masu fafutukar kawar da cin hanci a kasar sun fi sakewa karkashin gwamnatin da Buharin ya gada. Akwai shari'u da dama da suka danganci cin hanci wanda suka jima gaban kotu ba tare da yanke hukunci kansu ba. Najeriya a yanzu ta kasance kurar baya musamman ma idan aka yi la'akari da jerin kasashen da ke kan gaba wajen cin hanci da rashawa. Najeriya dai ita ce ta 148 daga cikin kasashe 180 a wancan lissafi da aka yi.

Lokacin da Buhari ya karbi mulkin Najeriya farashin danyen mai ya yi faduwar gwaron zabi a kasuwannin duniya kazalika ya samu an wawushe dukiyar kasar daga lalitar gwamnati sai dai a iya shekaru ukun da ya yi ya na mulki bai kai ga fidda wani tsari nagartacce da zai kai kasar ga daina dogaro da man fetur wajen samun kudin shiga ba. Wani abin dubawa har wa yau shi ne yadda Najeriya ke fuskantar matsalar man fetur a kai a kai duk kuwa da cewar shugaba Buharin ne ke jagorantar ma'aikatar man fetur din kasar. Kyautuwa ya yi a ce matsalar ta zama kan gaba amma akasin haka aka gani. Wannan ba zai rasa nasaba da faduwar da hannayen jarin a kasar ba bayan da ya furta cewar zai sake tsayawa takara.

 Ayar tambaya kan cewar ko Buhari zai iya yin wa'adin mulkin na biyu saboda rashin koshin lafiya?

 Thomas Moesch shugaban sashen Hausa na DW wanda shi ne ya rubuta wannan sharhi
Thomas Moesch shugaban sashen Hausa na DW wanda shi ne ya rubuta wannan sharhi

Yawan shekaru da karancin koshin lafiya na wani abin dubawa ne game da takarar ta Buhari domin lokacin da zai kammala wa'adinsa na biyu zai kasance ya na da shekaru 80. Najeriya na bukatar shugaban da ya ke da koshin lafiya da kuma kankantar shekaru wanda kuma zai aiwatar da abubuwan da ya sanya a gaba. Har yanzu Shugaban na da goyon baya a arewacin kasar inda Musulmi suka fi yawa sannan ya samu magoya baya da dama a yammacin kasar a zaben 2015 to sai dai da wuya kalubalen tsaro da ake fuskanta a tsakiya kasar ya iya sa shi samun nasara a yanki. Yanzu shawara ta rage ga masu zabe da kuma jam'iyyar PDP da ke adawa wadda ta fidda wanda zai goga da Buhari. Ya zuwa yanzu dai ba wannan dan takara a kasa.