1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sharhi: (Goyon baya): Babu zabi ga matakan soja

August 28, 2013

Bisa zargin cewa Siriya ta yi amfani da makamai masu guba kan fararen hula, ta ƙetare jan layin da Amirka ta zana. A dalilin haka, dole ne yamma ta ɗauki matakin soji a cewar Loay Mudhoon na DW.

https://p.dw.com/p/19Y9i

Hotuna masu sosa rai na gawawakin yara da mata da kuma na farar hula da suka samu munanan raunuka a cikin rikicin Siriya sun kau da shakkun da da ake bayyanawa game da yiwuwar daukar matakin sojin a kan gwamnatin Siriya.

Ko shakka babu rahotannin da aka samu daga kungiyar likitoci ta kasa da kasa wato "Doctors without Borders" wadda ta shafe shekaru tana aikin kafada da kafada tare da asibitocin sirri a kasar Siriya na tabbatar da ta'asar kisan kiyashin dake afkuwa a wannan kasa. Shugaban Amirka Barack Obama ya kira amfani da mugan makamai da ake yi wajen aikata kisan kare dangi a kasar ta Siriya tamkar wuce gona da iri.

An ƙetare "jan layi"

Za a ma tuna cewa a watan Agustan bara shugaban na Amirka ya bayyana wa duniya cewa shi sam ba zai zura ido ya ga ana amfani da makamai masu guba a yakin basasan Siriya ba. Da yake yanzu an samu daruruwan mutane da suka mutu da kuma dubbai da suka samu munanan raunuka za a iya cewa lokaci ya yi da za a ga aiki da cikawa daga shugaban na Amirka da ke zaman mutun mafi karfin iko a duniya. A don haka akwai yiwuwar daukar matakin soji na bai daya akan gwamnatin Siriya- matakin da Amirka za ta jagoranta nan da yan kwanaki. Shi dai shugaban na Amirka ba shi da wani zabi da ya wuce daukar wannan mataki.

Babu sauyi a rikicin

Bugu da kari bai dace ba kasashen yamma su bari a yi amfani da irin wadannan makamai a kasar ta Siriya ba, in har suna bukatar dakile kai hare-hare kare dangi nan gaba. Wannan dai abin takaici ne dubi da rashin hangen nesa a bangaren gwamnatin shugaba Asad da kuma gaskiyar cewa ita ce ke da runbum makamai masu guba mafi girma a yankin Gabas ta Tsakiya.

Bisa ga dukkan alamu za a dasa ayaoyin tambaya game da duk wata ayar tambaya da za a dasa a kan matakin soji da Amirka ke muradin dauka akan gwamnatin Siriya. Za a dasa ayan tambaya game da manufa ta siyasa dake tattare da daukar wannan takaitaccen mataki. Ko shakka babu a halin yanzu luguden wuta na kwanaki byu da ake sa ran yi akan sansanonin sojin Siriya zai janyo daukar matakin yin ramuwar gayya. Kuma hakan ba abu da zai kawo karshen zud da jini ba balle ya sauya iko da kuma tunanen bangarorin da ke cikin wannan rikici mai sarkakkiya ba.

Loay Mudhoon, Programmdirektion DW-RADIO/DW-WORLD / Islamexperte der deutschen Welle. Foto: Per Hendriksen / DW
Loay MudhoonHoto: DW

To sai dai duk da haka za a ci gaba da kyautata fatan cewa duk wani mataki da zai karya logon Assad zai tilasata komawa teburin tattaunawa. A don haka wajibi ne gamayyar kasa da kasa ta dauki matakan diplomasiya domin kawo dukan bangarorin da ke cikin rikicin kan teburin tattanawa musamman wadanda ke dasa da Assad da suka hada da China da Rasha da Iran dake marasa baya. Babbar matsala a nan ita ce matakin sojin da Amirka ke shirin dauka zai iya ba wasu kasashen damar shiga rikicin na Siriya .

Saboda cewa Rasha da China na nuna halinko in kula game da da dokokin da suka haramta yin amfani da makamai masu guba. Ana kuma bayyana damuwar cewa kifar da gwamnatin Asad ba zai kawo karshen yakin basasan kasar ta Siriya ba. A don haka hanya daya tilo da ta dace a bi don kawo karshen musibar dake faruwa a Siriya ita ce daukar matakin bai daya a bangaren gamayyar kasa da kasa.

Mawallafa: Loay Mudhoon / Halima Balaraba Abbas
Edita: Mohammad Nasiru Awal