1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sharhi: Assad da alƙawuransa na yaudara

March 28, 2012

Amincewar da Bashar al-Assad yayi ga shirin zaman lafiyar wakilin Majalisar Ɗinkin Duniya Kofi Annan ka iya zama wata yaudara, inji Daniel Scheschkewitz a cikin wannan sharhi.

https://p.dw.com/p/14TNo
epa03139216 A handout picture released by Syrian Arab News Agency SANA, shows Syrian President Bashar Al-Assad (R) listening to UN Arab League envoy Kofi Annan (L) during their meeting, at Syrian presidential palace in Damascus, Syria, 10 March 2012. Annan arrives in Damascus on 10 March and is expected to call for talks between the government and the opposition in a bid to end the year-long violence. EPA/SANA HANDOUT HANDOUT EDITORIAL USE ONLY/NO SALES +++(c) dpa - Bildfunk+++ pixel
Bayan lokaci mai tsawo Assad ya amince da shirin AnnanHoto: picture-alliance/dpa

Tsagaita buɗe wuta, janye sojoji daga yankunan 'yan adawa, aiwatar da sauye sauyen siyasa da sako dukkan firsinonin da aka tsare a lokacin bore, waɗannan su ne muhimman rukunan shirin zaman lafiyar Kofi Annan ga ƙasar Siriya, wanda shugaba Bashar al-Assad ya amince da shi bayan ya ɗauki wani lokaci. Shin ko da gaske shugaban mulkin kama karyar yake a wannan karo zai cika alƙawarin da ya ɗauka ko kuma yaudara ce kawai yake kamar yadda ya saba? Lokaci dai zai nuna.

Yaudara maimakon ba da kai

Ganin cewa kawo yanzu Bashar al-Assad bai cika dukkan alƙawuran da  ya ɗauka ba, a wannan karon ma a nuna shakku game da maganarsa. Maimakon ya aiwatar da canjin siyasa kamar yadda ya alƙawarta a watanni baya, ƙara ɗauka matakan danniya yayi akan 'yan adawa. Sau tari Assad ya nuna wa gamaiyar ƙasa da ƙasa shirin ba ta haɗin kai ba tare da an gani a ƙasa ba. Saboda haka wannan amincewar da yayi ga shirin zaman lafiyar Kofi Annan ka iya zama wata yaudara ganin cewa ba ya da wani zaɓi a dangane da halin da yake ciki yanzu. Tun bayan ziyarar farko da Annan ya kai a birnin Damaskus kimanin makonni biyu da suka wuce abubuwa sun canza. Gwamnati a Mosko ta fara nuna wa Assad yatsa sannan ta goyi bayan shirin zaman lafiyar na Majalisar Ɗinkin Duniya. A fili Rasha na ƙara matsa wa abokin ɗasawarta lamba.

Assad na ƙara zama saniyar ware

Ita ma China ta nuna shirin yin watsi da manufar turjiya da take ɗauka a kwamitin sulhu don goya wa shirin zaman lafiyar Kofi Annan baya. Ita ma Turkiya maƙociyar Siriya a farkon wannan mako ta katse duk wata hulɗar diplomasiya da Siriya. Yanzu dai Assad na ƙara zama saniyar ware a duniya. Bugu da ƙari Saudiyya da wasu ƙasashen yanki Golf sun fara tura wa 'yan tawaye da makamai, yayin da boren ke ƙara dannawa kusa da fadar mulki ta birnin Damaskus, inda ake zubar da jini. Wata majiya daga Mosko ta ce Assad ba ya da wani zaɓi face ya amince da shirin zaman lafiyar a hukumance.

In this image made from video, Syrian President Bashar Assad, second right, visits Baba Amr neighborhood in Homs, Syria, Tuesday, March 27, 2012. Assad visited Baba Amr, a former rebel stronghold in the key city of Homs that became a symbol of the uprising after a monthlong siege by government forces killed hundreds of people many of them civilians as troops pushed out rebel fighters. Homs has been one of the cities hardest hit by the government crackdown on the uprising that began last March. (Foto:Syrian State Television via APTN/AP/dapd) SYRIA OUT TV OUT
An Assad da rashin cika alƙawariHoto: Syrian State Television/AP

Sai dai hakan ba ya nufin an ɗauki matakan aiwatar da shirin. Musamman a ɓangaren 'yan adawar Siriya babu wanda ya yi amannar cewa a wannan karo Assad zai cika alƙawarin da ya ɗauka. Kawo yanzu mutane 9000 suka mutu a rikicin kuma a kullum yawansu yana ƙaruwa ne. Ga 'yan tawayen dai kawo ƙarshen yaƙin ba tare da Assad ya sauka daga kan karagar mulki ba, ba kyakkyawan zaɓi ba ne. Saboda haka ake shakka ko za su amince da tsagaita wutar ba tare da farko sun samu wani ihisani daga gwamnati ba.

Shakku akan halaiyar 'yan adawa

Kofi Annan ya na son a aika da wata tawagar sa ido ta Majalisar Ɗinkin Duniya wadda za ta sa ido akan shirin zaman lafiyar. Amma ka da a manta tawagar sa ido ta ƙasashen Larabawa ta gaza wajen dakatar da zubar da jini a Siriya. Ko da yake tawagar ta Majalisar Ɗinkin Duniya za ta kasance babba kuma mai kayan aiki na zamani amma ba za ta iya ceto ƙasar daga faɗawa yaƙin basasa gadan-gadan ba, idan gwamnati da 'yan adawa ba su ba da cikakken haɗin kai ba. Assada zai so ya ci gaba da yaƙi domin ya ci gaba da mulki. Su ma 'yan adawa, bisa rahotannin ƙungiyoyin kare hakkin bil Adama, sun aikata ta'asa da yawa. Kiristoci da 'yan ɗarikar Alawi ta Assad, na tsoron cewa ana iya ɗaukar fansa akansu. Yaƙin basasan dai ya ƙara raba kawunan 'yan Siriya sannan ƙasashen duniya na shakku game da halaiyar 'yan adawa.

In this citizen journalism image taken on Monday March 26, 2012 and provided by Edlib News Network ENN, anti-Syrian regime protesters shout slogans during a demonstration in Binish town in Idlib province, northern Syria. Syrian forces have fired shells at a central city that has come to symbolize the anti-government uprising, activists said, while the country's Muslim Brotherhood branch said it would work for a democratic state if President Bashar Assad falls. The Arabic banner in the background reads: "To who it may concern, the revolution's court will not forgive anyone". (Foto:Edlib News Network ENN/AP/dapd) THE ASSOCIATED PRESS IS UNABLE TO INDEPENDENTLY VERIFY THE AUTHENTICITY, CONTENT, LOCATION OR DATE OF THIS HANDOUT PHOTO
'Yan adawa ba su yarda da alƙawarin Assad baHoto: Edlib News Network ENN/AP

Assad ya samar wa kansa lokaci biyo bayan amincewar da yayi. Aikin samar da zaman lafiya na Kofi Annan zai ci gaba da zama wani jan aiki.

Mawallafa: Daniel Scheschkewitz/Mohammad Nasiru Awal
Edita: Zainab Mohammed Abubakar

Tsallake zuwa bangare na gaba Bincika karin bayani

Bincika karin bayani