1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Share fagen kamfe a Chadi

Abdou Gazali Mahman/YBMarch 10, 2016

Bayan shekaru 26 a kan mulki shugaba Idriss Deby zai fafata da 'yan takara 13 a watan Afrilu. Zaben da 'yan adawa musamman bangaren matasa ke cewa suna bukatar sauyi.

https://p.dw.com/p/1IATo
Tschad Präsident Idriss Deby
Shugaba Idriss DebyHoto: picture-alliance/dpa/C. P. Tesson

A kasar Chadi lokacin da ya rage wata guda a gudanar da zaben shugaban kasa 'yan takara sun soma kafa kwamitocin na masu goyon bayansu musamman mata da samari kafin zuwa ranar soma yakin neman zabe ta 20 ga wannan wata na Maris.

Wasu matasa masu goyan bayan 'yan adawa a cikin birnin Ndjamena na gudanar da taruka na nuna kosawarsu da mulkin shugaba Idriss Deby a dai dai lokacin da ake shirye-shiryen gudanar da zaben shugaban kasa a kasar. Ilahirin 'yan takarar ne dai na bangaren 'yan adawa da na masu mulki suka dukufa wajen zawarcin 'yan kasar musamman matasan maza da mata domin su shigo kwamitocin da jam'iyyun nasu suka fara kafawa domin kintsawa kafin zuwa ranar 20 ga wannan wata na Maris da za a bude yakin neman zabe.

Frederic Doumyohol Dillah shi ne babban sakataren kwamitin goyan bayan dan takarar jam'iyyar MPS ta shugaban kasa Idriss Deby:

Tschad N'djamena Saleh Kebzabo (L) and Ngarlejy Yorongar
Saleh Kebzabo(Hagu) da Ngarlejy Yorongar (dama) daga bangaren adawa na jinjina ga magoya baya a N'djamenaHoto: Getty Images/AFP/G. Cogne

"Babban aikin da musa adawa ke yi shi ne jawo hankalin matasa na su kawo goyan bayansu ga jam'iyyar Mouvement Patriotique du Salut wato MPS ta shugaban kasa. Domin shugaban Idriss Deby ya yi an gani an yaba, dan haka muke son sake ba shi wani sabon wa'adin mulkin na shekaru biyar domin a matsayinmu na matasa hankalinmu ya kwanta a zamaninsa kuma mun yi imanin a nan gaba zan iya yin abin da ya yi a baya".

Sai dai shugaban kwamitin zartarwa na matasa na jam'iyyar Action Populaire pour la Solidarite et L' unite de la Rep Jules Daniel Yohounkilam ya ce lokaci ya yi na a samu sauyi a kasar Chadi kuma suna fatan hakarsu za ta cimma ruwa a wannan karo:

"Ba za mu iya ci gaba da jurewa rayuwa da wannan mulkin na kama karya ba a tsawon shekaru 25. Lokaci ya yi da ya kamata matasan Tchadi sun farka su jibinci makomar wannan kasa"

Tschad - N'DJAMENA
Al'umma a birnin N'djamenaHoto: Getty Images/M. Di Lauro

Ita ma dai jam'iyyar UNDR ba a barta baya ba wajen kokarin hada kai da matasan domin cimma burinta a zaben na wannan karo.Kuma Gebdanbe Ouateure Epaphras mamba a komitin gudanarwa na jam'iyyar ya yi karin bayani kan burin da jam'iyyar tasu take da kan matasan da kuma abin da take jira daga garesu:

"Wannan kwamiti namu na taimakawa matasan jam'iyyar ta hanyar basu horo. Kuma a ko yaushe suna mike a sahun gaban harakokin jam'iyyar domin shawo kan matsalolin matasa na daga cikin burin wannan jam'iyya tamu ta UNDR"

A ranar 10 ga watan Afrilu ne dai idan Allah ya kaimu za a gudanar da zaben shugaban kasar inda shugaba mai ci Idriss Deby wanda ke kan karagar mulkin kasar ta Chadi shekaru 26 zai fafata da wasu 'yan takara 13.