Shakku kan makomar Boko Haram | Siyasa | DW | 01.08.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Shakku kan makomar Boko Haram

A Najeriya karuwar kai hare-haren kungiyar Boko Haram bayan samun sauki na watanni, na haifar da damuwa ga mazauna yankin arewa maso gabashin Najeriya, ana dai ganin akwai bukatar sabon lale na yakar kungiyar da gaske.

Kama daga hare-haren da aka kai a jami'ar Maiduguri zuwa ga na garin Dikwa da harin kwanton baunana da aka yiwa masu aikin binciko man fetir a jihar Borno, lamari ne da ke haddasa alamar tambaya a zukatan al'umma da ma shakku na gudun sake komawa gidan jiya bayan alwashi na murkushe kungiyar. Malam Kabiru Adamu masani a kan harkokin tsaro a Najeriya, ya ce:

" Na farko an samu canjin yanayi na damuna, sojoji basu iya sarrafa na'urorin yaki kan 'yan tadda yadda ya kamata, akwai matsalolin yabanya da ke ba wa 'yan taddan damar buya. Sannan akwai samun raunin bayanan sirri wanda ke da nasaba da sauya shugabancin sojojin da aka yi".

To sai dai bayanan da ke dfitowa daga bakin rundunar sojojin Najeriyar na karo da juna, wanda ke jefa shakku a zukatan alu'mmar kasar a kan yadda tafiyar take a yanzu. Dr. Abubakar Umar Kari, masanin yanayin zamantakewar al'umma da ke jami'ar Abuja na ganin akwai kyakyawar fata anan gaba.

"Wannan abinda ke faruwa ba abu ne da ba za'a iya shawo kansa ba, wajibi ne gwamnati ta hada kan shugabannin dukkanin bangarorin da ke zaman doya da manja a kasar dan samun fahimtar juna."

Fuskantar koma baya na bullar sabin hare-hare na ta'adanci a Najeriyar ya sanya tambayar ko akwai bukatar sake lale ne ga daukacin lamarin? Har ila yau ga Malam Kabiru Adamu.

"Akwai bukatar a waiwayi dukmkanin inda ake samun tangarda, rundunar sojin Najeriya tana kame wasu yankuna amma basa rikewa da kyau."

A yayinda manyan hafoshin sojin Najeriya suka koma da aiki a Maiduguri bisa umurnin mukadashin shugaban kasar Najeriyar Yemi Osinbanjo, al'ummar kasar na ci gaba da fata ta samun sauki da ganin sauyi cikin hanzari daga hare-haren da ke jefa tsoro a zukatansu.