1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kokarin kawar da gwamnatin Venezuela

Usman Shehu Usman YB
January 29, 2019

A ci gaba da kokarin da Amirka ke yi na kifar da gwamnatin Nicolas Maduro a Venuzuela. Amirka ta sanar da jerin takunkumi kan kadarorin kasar, musamman kamfanonin mai da kasar ke dogara da su.

https://p.dw.com/p/3COVj
Venezuela, Caracas: Nicolas Maduro hält eine Ansprache
Hoto: Reuters/Miraflores Palace

Bisa sabbin takunkuman da Amirka ta kakaba wa Venezuela, kasar za ta yi asarar Dalar Amirka biliyan bakwai yayin da kasar ta Amirka ke ci gaba da kokarin mayar da gwamnatin Maduro saniyar ware a harkokin siyasar duniya. Sai dai a martaninsa shugaban kasar Venezuela Nicolas Maduro ya bayyana cewa wadannan matakan da Amirka ta dauka haramtattu ne a bisa ka'idojin kasa da kasa. Kuma ya ce ba wai Amirka na yin haka don tausayin 'yan kasar ba llla kawai so take ta kwace arzikin da Allah ya hore wa Venezuela.

A yanzu haka dai madugun 'yan adawar Venezuela Juan Guaido, wanda ya ayyana kansa a matsayin shugaban kasa, ya kara jajircewa don bijere wa umarnin hukumomin Caracas inda yake kokarin shinfida nasa mulkin. Kuma Guaido ya lashi takwabin ci gaba da jagorantar bore a kasar.

Venezuela Juan Guaido besucht Gottesdienst in Caracas
Juan Guaido na ci gaba da neman hadin kan kasa da kasaHoto: Imago/Agencia EFE/M. Gutiérrez

To sai dai yayin da madugun 'yan adawar ke ci gaba da yunkurin samun goyon bayan kasashen duniya, manyan kasashe kamarsu Rasha da Turkiyya da China, sun ci gaba da goyon baya ga Nicolas Maduro a matsayin shugaban kasa, yayin da Rasha ke gargadin Amirka bisa yin katsalandan a Venezuela. Ita ma China ko da a safiyar Talata ta kara jaddada goyon bayanta ga gwamnatin Venezuela, inda kakakin ma'aikatar harkokin wajen Chaina ya fada wa manema labarai.

Yayin da kasar ta Amirka ke kara dagewa wajen ganin bayan gwamnatin Maduro shi kuwa shugaban kasar ta Venezuela ya ci gaba da jan damarar tunkarar duk abin da ka iya biyo baya. A kan batun yanke huldar Venezula da Amirka Maduro ya ce a shirye yake ya kafa wani ofishin tuntuba tsakanin kasarsa da Amirka, domin akwai irin wannan ofishin tsakanin Amirka da Kuba, kuma ya ce yanzu shekaru 50 Amirka da Kuba ba jakadun kasashe tsakaninsu amma irin wadannan ofisoshin su ne ke aiki a matsayin na tuntuba tsakanin kasashen biyu.