Shagulgullan salla ƙarama a ƙasashen musulmi na dunia | Labarai | DW | 22.10.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Shagulgullan salla ƙarama a ƙasashen musulmi na dunia

Da dama daga ƙasashen musulmi a dunia, a na gudanar da shagulgullan salla Idil-Fitri, kokuma Sallah ƙarama a yau lahadi, bayan wata guda na ibadar azumin ramadan, saidai kamar ko wace shekara abana ma, ba ayi sallar ba, bai ɗaya, a dukkan kasashen musulmi.

A kasashen yankin Golf, da su ka haɗa da Saudi Arabia, Bahreim, Qatar, da Koweit sai gobe idan Allah ya kai,za su gudanar da salla.

A kasashen Nahiyar kamar Nigeria da Niger, a yanzu haka a na ci gaba da shagulgullan bayan hawan idi.

Albarkacin wannan rana shugaban ɗarikar roman katolika, Paparoma Benoit na 17, ya issar da saƙwan taya murna ga musulmin dunia.

Paparoma, yi kira musulmi da kristocin dunia, su yi addu´o´i ga Iraki, na neman Allah ya maido da zaman lahia a wannan ƙasa da ke fama da tashe-tashen hankulla.

Hatta yan ƙunar baƙi wake, sun kai ƙarin hare-hare, wanda su ka sanadiyar mutuwar mutane da dama.