Sepp Blatter ya yi tazarce a kan FIFA | Labarai | DW | 29.05.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Sepp Blatter ya yi tazarce a kan FIFA

Sepp Blatter ya lashe zaben shugabancin hukumar kwallon kafa ta FIFA bayan da abokin hamayarsa na Kasar Jodan ya janye takararsa.

Shugaban hukumar kula da wasannin kwallon kafa ta duniya Sepp Blatter ya yi nasarar sake yin tazarce bayan da ya lashe sakamakon zaben da aka gudanar a ranar Juma'a a cibiyar hukumar ta FIFA da ke a birnin Zurick na kasar Swizerland.Sepp Blater dan shekaru 79 ya lashe zaben ne bayan da abokin karawarsa na Kasar Jodan Ali Ben Hussein ya janye takarar tasa a daidai lokacin da ake shirin zuwa zagaye na biyu.

Wannan dai shi ne karo na biyar da Sepp Blatter ke yin tazarce akan kujerar shugabancin hukumar ta FIFA.

Sake zaben Sepp Blatter ya zo ne a daidai lokacin da hukumar ta FIFA ke fama da rikicin badakalar cin hanci wanda ya kai ga kulle wasu daga cikin mambobinta.Daga yanzu zai ci gaba da shugabancin hukumar ta FIFA a wani sabon wa'adin na shekaru hudu a nan gaba