Sentsov ya samu kyautar kare hakkin dan adam | Labarai | DW | 25.10.2018
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Sentsov ya samu kyautar kare hakkin dan adam

Majalisar Tarayyar Turai ta ba da kyautar Sakhrov mai daraja na kare hakkin dan adam ga Oleg Sentsov mai shirya fina-finai da ke daure a gidan yari.

Sentsov mai shekaru 42 an haisfeshi a birnin Simferopol da ke cikin yankin Kirimiya, ya yi fafutukar ganin an sako fursunonin siyasar Ukraine da ke daure a Rasha. Matashin ya shahara wajen sukar gwamnatin Rasha kan mamaye yankin Kirimiya da karfin tuwo.

Wannan ya bashi damar shiga sahun mutane uku da suka haye mataki na karshe a cin kyautar, ciki har da wasu kungiyoyi 11 masu ceto 'yan ci rani a teku, tare da Nasser Zefzafi jagoran gwagwarmayar kwato 'yanci a Maroko da ya shafe shekaru 3 a daure.

Kyautar Sakharov na zuwa da tukuicin kudi na dala dubu hamsin, Nelson Mandela shi ne mutum na farko da ya taba lashe kyautar tun bayan da aka soma bayarwa a shekarun 1988.