Senegal ta rufe zirga-zirga jiragen sama | Labarai | DW | 17.03.2020
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Senegal ta rufe zirga-zirga jiragen sama

Duban matafiya galibi 'yan yawan shakatawa ta rutsa da su a filin saukar jiragen na Senegal sakamakon, dokar da gwamnatin ta Senegal ta zartas na dakatar da zirga-zirga ta jiragen sama.

Gwamnatin ta Senegal ta dau wannan matakin na dakatar da zirga-zirga jiragen sama tsakaninta da kasashen Faransa da Italiya da Portugal da Beljiyam da Tunisiya da kuma Aljeriya domin dakile yaduwar cutar Coronavirus. Ministan sufiri na kasar Alioun Sarr ya ce dokar za ta yi kwanaki 30 tana aiki har sai al'amura sun fara daidaita. Senegal na daga cikin kasashen Afirka inda cutar ta Coronavirus ta bayyana wanda kawo yanzu ake da kusan mutane 27 da suka kamu da ita.