Senegal ta rufe iyakarta da Guinea | Labarai | DW | 22.08.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Senegal ta rufe iyakarta da Guinea

Kasar Senegal ta kasance kasa ta baya-bayan nan daga cikin kasashen Afirkan da suka takaita zirga-zirga sakamakon barkewar cutar Ebola

Kafofin yada labaran Senegal suka rawaito cewa, kasar ta rufe iyakarta da kasar Guinea wace ke makotaka da ita. Ministan ckin gidan kasar Abdoulaye Daouda Dallo ya ce wannan doka ta shafi jiragen sama da na kasa, kuma dakarun sojin kasar za su tabbatar da cewa an kiyaye wannan doka yadda ya kamata.

Wannan mataki na Senegal na zuwa ne jim kadan bayan da mahukuntan Afirka ta Kudu suka haramta wadanda ba 'yan kasa ba shigowa kasar daga duk wata kasar da ke fama da cutar ta Ebola abin da shirin samar da abinci na duniya ko kuma World Food Programme a turance, ta ce ya janyo matukar koma baya ga tattalin arziki da kuma shirin samar da abinci.

Dokar dai ta tanadi yin tambayoyi wa duk dan asalin Afirka ta Kudun da ya fito daga Guinea, da Liberia da Saliyo da Najeriya, kuma ma idan har akwai bukata, tilas ne a yi musu gwajin lafiya kafin su sami damar shiga kasar.

Mawallafiya: Pinado Abdu Waba

Edita: Umaru Aliyu