Senegal na ci gaba da tsare Habre na Chadi | Siyasa | DW | 01.07.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Senegal na ci gaba da tsare Habre na Chadi

Kotun musamman za ta gurfanar Hissene Habre bisa zargin kashe mutane 40.000 lokacin da ya mulkin Chadi. Tun a ranar lahadi Hukumomin Senegal suka tsare tsohon Shugaban mai shekaru 70 a duniya.

Mahukuntan kasar ta Senegal sun cafke Hissene Habre kasa da sa'o'i 72 bayan ziyarar da Shugaban Amirka Barack Obama ya kai zuwa kasar ta Senegal. Shugaban ya na goyon bayan shirin gabatar da Habre a gaban kotu, bisa dokokin Senegal, kamar yadda taron musamman na shugabannin Afirka ya cimma. Habre ya kwashe shekaru 22 ya na rayuwa babu wata tsangwama a Senegal, yayin da kungiyoyin kare hakkin dan Adam ke zargin Habre da hallaka kimanin mutane 40,000 a tsawon mulkinsa na shekaru takwas, kafin kawar da shi daga madafun iko a shekarar 1990.

Jacqueline Moudeina Trägerin Alternativer Nobelpreis 2011 Besuch bei DW Bonn

Lawya Moudeina na kokarin kwaco wa 'yan Chadi hakkinsu

Hissene Habre wanda ya kwace madafun ikon kasar ta Chadi cikin shekarar 1982, yanzu yana da shekaru 70 da haihuwa, kuma gwamnatocin Senegal da suka gabata, sun yi watsi da duk wata bukata ta kama shi. Sai dai kuma sabon shugaban Senegal Macky Sall ya cimma yarjejniya da kotun kasa da kasa da ke kasar Holland, wace ta samar da kudi da kuma kayan aiki da ake bukata domin gudanar da shari'ar Habre a Senegal. Babacar Gueye masananin harkokin shari'a na jami'ar Cheick Anta Diop da ke birnin Dakar ya nuna goyon baya da wannan mataki na hukunta Habre a wannan lokaci:

"Matakan suna kan ka'ida, saboda ya dace a hukunta shi, kuma muddun haka zai kasance, sai an kama shi. Saboda a tsare shi kamar yadda matakan shari'a suka tanada."

Lawyoyin Habre na da ja game da hanyoyin da aka bi wajen tsareshi

A daya hannun lauyoyin da ke kare tsohon Shugaban kasar ta Chadi Hissene Habre, sun nuna rashin gamsuwa da matakan da aka bi wajen kama shi a wannan lokaci:

''Mai gabatar da kara na musamman ya kai ziyara zuwa birnin N'Djamena na kasar Chadi, inda ya gudanar da bincike, kuma ake da sakamakon abin da aka gano.''

Amma Bubakar Gueye masanin shari'ar ya amince da hanzarin da lauyoyin na Habre suka gabatar na nuna damuwa da kamun a wannan lokaci. Kuma daya daga cikin lauyoyin ya ce haka ya zama garkuwa da mutumin da yake karewa:

Tschad Präsident Idriss Dedy Itno

Shugaba Dedy Itno ne ya hambarar da Habre a kujerar mulki

''Lauyoyin suna da hujjar korafi, saboda yadda aka yi lamarin cikin gaggawa, amma ina gani, idan aka lura da yanayin da ake ciki, haka shi ne mafi dacewa.''

Kungiyar kare hakkin dan Adam ta Human Right Watch wadda ta tattara bayanai a kan mutanen da kan ta'asan da Hissene Habre ya aikata lokacin da yake mulki, ta shaida wa Kamfanin dillancin labaran Jamus cewa ya yi bayan shekaru 22 wadanda suka gamu da azaba yayin mulkin na kama karya za a kwato musu hakkinsu.

Zai kai zuwa shekara ta 2014 ko 2015 kafin kammala duk abin da ake bukata na hukunta Habre. Ana sa ran masu gabatar da kara za su nemi ci gaba da tsare shi har lokacin da za a gudanar da shari'ar. A farkon wannan shekara ne aka kaddamar da kotun ta musamman wadda za ta yi shari'ar Hissene Habre a kan take hakkin dan Adam a kasar ta Chadi lokacin da yake rike da madafun iko.

Mawallafi: Suleiman Babayo
Edita: Mouhamadou Awal Balarabe

Sauti da bidiyo akan labarin