Senegal: Hana maido mamata a gida | Labarai | DW | 07.05.2020
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Senegal: Hana maido mamata a gida

Hukumomi a Senegal za su ci gaba da hana shigowa da gwarwakin 'yan kasar da suka hallaka a waje sakamakon kamuwar da suka yi da cutar Covid-19.

Wata kotu a birnin Dakar ta yi watsi da bukatar da wasu dangin mamatan suka shigar a gabanta domin basu hurumin dawowa da gawakin da suka makkale a kasashen Amirka da nahiyar Turai.

Sai dai jama'ar da suka shigar da karar sun nuna rashin jin dadinsu game da matakin da kotun na watsi da bukatarsu bisa fargabar sake yada cutar coronavirus.

Tun daga farko dai lauyoyyin jama'ar dai sun shigar da kara ne a gaban kotun kolin, suna masu zargin gwamnati da taka hakin zartar da addini ga 'yan kasar da suka rigamu gidan gaskiya, wadanda danginsu suka ce za su yiwa jana'i'za irin ta Islama.