1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Senegal: Gangamin goyon bayan jagoran adawa

Abdullahi Tanko Bala
March 15, 2023

Dubban jama'a sun fita titunan Dakar domin nuna goyon baya ga jagoran adawa Ousmane Sonko duk da haramcin hakan da hukumomin kasar suka yi

https://p.dw.com/p/4Ok1b
Senegal Dakar | Proteste
Hoto: Sylvain Cherkaoui/AP/picture alliance

Gangamin dai somin tabi ne na jerin zanga zangar da aka shirya don nuna goyon baya ga Sonko.

Magoya bayansa sun ce tuhumar da ake yi masa ta zargin bata suna da kazafi, yunkuri ne na gwamnati mai ci domin dakile siyasar sa ciki har da neman hana masa takarar shugaban kasa a 2024.

Shugaban Senegal dai Macky Sall har yanzu bai fito fili ya baiyana ko zai sake tsayawa takarar shugabancin kasar a 2024 ba, haka kuma bai musanta rade-radin da ake yi cewa zai tsaya takara ba.

Senegal wadda ke zama zakaran gwajin dafi na dimukuradiyya a yammacin Afirka dokokin kasar sun bada dama ne ga shugaban kasa ya yi wa'adin mulki sau biyu na shekaru biyar biyar.