Seleka ta dara Afirka ta Tsakiya gida biyu | Labarai | DW | 18.08.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Seleka ta dara Afirka ta Tsakiya gida biyu

Mayakan tsofuwar kungiyar tawaye ta Seleka sun sanar da dara Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya gida biyu, inda suka ayyana birnin Birao a matsayin babban birnin kasar .

Rahotanni daga yankin arewacin Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya sun ce kungiyar Seleka ta tsofoffin 'yan tawayen kasar ta fitar da sanarwar kafa sabuwar kasa mai suna Dar El Kouti. Tuni aka nada Michel Djotodiya tsofon shugaban kasar na mulkin soja a matsayin sabon shugaban kasar ta Dar El Kouti, da kuma gwamnatin wannan sabuwar kasa mai membobi akalla 11 na rikon kwarya.

Birnin Birao dake a nisan kilometa 800 da Bangui babban birni na a matsayin babban birnin wannan sabuwar kasa ta Dar El Kouti. Sanarwar tace matakin zai fara aiki ne daga lokacin da aka wallafa wannan sabuwar gwamnati, kuma za'a sanar da kasashen duniya wannan mataki na dara Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya gida biyu.

Sai dai wasu daga cikin rassan na Seleka da kuma gwamnatin kasar sun karyata wannan labarin.

Mawallafi: Salissou Boukari
Edita : Mouhamadou Awal Balarabe