Seleka da Anti-Balaka za su tsagaita wuta | Labarai | DW | 24.07.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Seleka da Anti-Balaka za su tsagaita wuta

Bangarorin da ke gaba da juna a Jamhuriyar Afirka ta tsakiya sun amince da shirin tsgaita bude wuta tsakaninsu a taron sulhu da ke gudana a birnin Brazaville na Kwango.

Mayakan sa kai na kungiyar Anti-Balaka da kuma 'yan tawayen Seleka ta Jamhuriyar Afirka Afrika ta Tsakiya sun rattaba hannu kan yarjejeniyar tsagaita wuta, da nufin kawo karshen fadan da aka shafe watanni ana fama da shi tsakanin Musulmi da Kiristocin kasar. Bangarorin biyu sun cimma wannan matsaya ne a birnin Brazaville na Kwango bayan da 'yan tawayen Seleke suka jingine bukatarsu ta dara jamhuriyar Afirka ta Tsakiya gida biyu domin musulmi su samu inda za su rayu ba tare da fitina ba.

Tun dai bayan da 'yan tawayen Seleka suka hambarar da gwamnatin Francois Bozize a watan maris na 2013 tare da dora Michel Djotodia wanda musulmi ne a kan karagar mulki, Jamhuriyar Afirka ta fada cikin rikici. Daidai da daukin da sojen faransa da kuma na kasashen Afirka suka kai bai bayar da damar shawo kan wannan rikici ba. Dubban mutane ne dai suka rasa rayukansu a wannan kasa yayin da kusan wasu karin miliyan guda suka kaurace wa gidajensu.

.

Sai dai kuma ana ganin cewar har yanzu ba arabu da bukar ba saboda kungiyar 'yan tawaye ta Seleka ta dare gida biyu. yayin da kungiyar 'yan bindigan sa kai ta Anti Balaka ta kasa samun sabon shugaba.

Mawallafi: Mouhamadou Awal Balarabe

Edita: Umaru Aliyu