1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Scotland na jiran sakamakon kuri'ar raba gardama

Pinado Abdu WabaSeptember 18, 2014

Yankin Scotland da ke hankorin samun 'yanci daga Birtaniya, ta kada kuri'ar raba gardamar da ta dauki tsawon lokaci tana daukar hankalin jama'a

https://p.dw.com/p/1DFNE
Schottland Referendum 18.09.2014
Hoto: Reuters/Paul Hackett

Scotland ta yi zaben da zai bayyana ko za ta cigaba da tsayawa cikin Birtaniya ko kuwa za ta kawo karshen dangantakarsu ta shekaru 307 da zama 'yantacciyar kasa mai cin gashin kanta a zaben raba gardamar da bisa dukkan alamu sakamakon shi zai tasiri sosai a siyasar yankin.

Kama daga mazauna tsibirai da tsaunuka zuwa birane kamar Glasgow, kawunansu sun rabu dangane da kuri'ar da ke daukar hankalin kawayen Birtaniya da masu zuba jari da ma kasashen da ke fama da rigingimu.

Duk da cewa sai safiyar juma'a ake sa ran samun sakamakon wannan zabe, kuri'un farko na nuna cewa wadanda ke goyon bayan yankin ya cigaba da kasancewa tare da Birtaniya na da tsakanin kashi 51 zuwa 53 cikin 100 na kuriun.

Da yawa na ganin cewa jama'a yanke hukuncin ne da zuciya ba da ka ba, wato ba tare da la'akari da abin da ka iya biyo baya a zahiri ba musamman wajen dangantaka da kasashe da ma tattalin arziki.

Shugabanin Turai da dama na ganin cewa bai kamata bayan gina Turai a rika samun wadanda suke so su balle ba, shi ya sa ma shugaban kasar Faransa Francois Hollande ya ce sakamakon wannan zaben ba makomar Birtaniya kadai ya shafa ba, har ma da na Turai.

*