1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

SCHRÖDER YA GANA DA CHIRAC A PARIS

YAHAYA AHMEDMarch 16, 2004

Kwanaki 5 bayan harin bamabaman da aka kai a birnin Madrid, shugaban gwamnatin tarayyar Jamus Gerhard Schröder, ya kai wata ziyara a birnin Paris yau, inda ya gana da shugaba Chirac na Faransa a fadar Elysee.

https://p.dw.com/p/BvlG
Shugaba Chirac da shugaba Schröder a fadar Elysée a birnin Paris
Shugaba Chirac da shugaba Schröder a fadar Elysée a birnin ParisHoto: AP

Kafin harin bamabaman da aka kai a birnin Madrid, masu tsara shirye-shiryen taron koli tsakanin shugaba Jacques Chirac na Faransa da shugaban gwamnatin tarayyar Jamus Gerhard Schröder, ba su yunkuri canza ajandar taron ba, tun da sun saba da tsara ta, har ma ta kusan zame musu jiki. Amma labarin wannan mummunan harin, da kuma sakamakon ba zato ba tsammanin da aka samu a zaben da aka yi a kasar Spain, sun tilasa wa jami’an diplomasiyyan yi wa shirin da suka tsara kwaskwarima.

Batun kalubalantar da `yan ta’adda ke yi wa harkokin tsaro a nan Turai dai ya janyo hauhawar tsamari a duk kafofin kula da kare lafiyar jama’a a manyan biranen nahiyar. Sabili da haka ne ma, ministan harkokin wajen Faransa, Dominique de Villepin, ya yi kira jiya litinin ga wani taron gaggawa na shugabannin Kungiyar Hadin Kan Turai da kuma kwamitin sulhu na Majalisar dinkin Duniya, don su tattauna yadda za su kirkiro sabbin matakai na kasa da kasa, da gurin magance barazanar da ‘yan ta’adda ke yi wa duniya a halin yanzu. Gwamnatin Faransan dai, ta dau wani matakin radin kai, na girke karin jami’an tsaro da shirin ko ta kwana, a tashohin jiragen kasa da na saman kasar. A wasu wuraren ma, an tura sojoji don su mara wa `yan sanda baya wajen magance duk wani rikicin da zai iya kunno kai. Har ilya yau dai, mahukuntan na birnin Paris, sun kuma kafa takunkumin hana jiragen sama, wucewa a wuraren da wasu muhimman masana’antu da kafofin makamashin nukilyan kasar suke. Duk da wadannan matakan kuwa, ministan tsaron Faransan, Nicolas Sarkozy, ya sake nanata cewa babu wata barazanar da `yan ta’adda ke yi wa kasarsa.

Daya muhimmin jigon da shugabannin Jamus da Faransa suka tattauna a kansa kuma, ya shafi sauyin da aka samu ne a karagar mulkin kasar Spain, da kuma yadda hakan zai shafi tafiyad da huldodi a kungiyar Hadin Kan Turai. Tuni dai, sabon Firamiyan kasar mai jiran gado, José Luis Rodriguez Zapatero, ya bayyana cewa, zai janye daga sahun masu goyon bayan manufofin shugaban Amirka George W. Bush, a nan Turai. Zai fi gwammacewa ne da bin manufofin da biranen Paris da Berlin suka sanya a gaba. A zahiri dai, abin da masharhanta ke zato shi ne, wannan canza shekar da kasar Spain ke niyyar yi, zai iya janyo amincewar kasashen Kungiyar Hadin Kan Turai da sabon kundin tsarin mulkin nahiyar, wanda a da can, saboda daddagewar da gwamnatin Firamiya Aznar mai barin gado ke yi masa, ake hasashen cewa ba zai sami karbuwa ba.

Shugaba Chirac da Schröder dai, ba su ba da tabbacin cim ma daiodaito kan wannan batun a taron kolinsu, ko kuma na shugabannin Kungiyar Hadin Kan Turan da za a yi nan ba da dadewa ba. Amma masu sukan lamiri na kyautata zaton cewa, bayan jayayyar da aka yi ta yi kan kundin tsarin mulkin a watannin baya, yanzu dai bisa dukkan alamu, za a sami wani gagarumin ci gaba, a yunkurin da ake yi na cim ma yarjejeniyar amincewa da shi a duk kasashen kungiyar.