Sauyin shugabanci a China | Labarai | DW | 05.03.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Sauyin shugabanci a China

Majalisar dokokin China za ta amince da Xi Jingping a matsayin sabon shugaba kasa yayin zaman da za ta fara a wannan Talatar.

Mambobin majalisar dokokin kasar China wadanda yawansu yakai dubu ukku daga jam'iyyar National People's Congress za su fara zamansu na tsawon makonni biyu a wannan Talatar. A lokacin zaman ne kuma majalisar za ta dauki mataki dangane da batun sauyin hannun mulki cikin shekaru goman da suka gabata, wanda suka nuna alamun yin haka tun cikin watan Nuwamban bara. A yayin zaman ne majalisar za ta ayyana sunayen wadanda za su rike manyan mukamin gwamnati, kana Xi Jingping kuma ya kammala shirinsa na darewa bisa kujerar shugabanbcin kasar. Kazalika, a lokacin zaman ne majalisar za ta bayyana irin alkiblar da tattalin arzikin kasar ta China za ta sanya a gaba, game da sanar da kasafin kudin kasar.

Mawallafi : Saleh Umar Saleh

Edita : Umaru Aliyu