Sauyin sheka a Najeriya | Labarai | DW | 28.10.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Sauyin sheka a Najeriya

Shugaban majalisar wakilan Najeriya Aminu Waziri Tambuwal ya sauya sheka daga jam'iyyar PDP mai mulki zuwa jam'iyyar adawa ta APC.

Sauya shekar dai zai kasance cike da kalubale a kan shugabancin majalisar da yake yi a yanzu musamman ganin cewar a yanzu jam'iyyar PDP ce ke da rinjaye a majalisar. Wakilinmu Uwais Abubakar Idris ya ruwaito cewar tuni Tambuwal ya dage zaman majalisar har zuwa watan Disamba abinda ake wa kallon dabara ce ta kaucewa fuskantar tsige shi daga wannan mukami. Matakin da ya dauka ya kawo karshen jita-jitar da kuma zaman jiran da aka dade ana yi a kan batun sauya shekar ta sa da ma yi wuwar tsayawar sa takarar gwamna a jami'yyar APC da ke mulki a jiharsa ta Sokoto.

Mawallafi:Uwais Abubakar Idris/LMJ
Edita: Abdourahamane Hassane