Sauya salon tsaro a Najeriya | Siyasa | DW | 04.12.2019
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Sauya salon tsaro a Najeriya

A cigaba da kokarin neman kawo karshen matsalar rashin tsaron da ke zama ruwan dare gama duniya a tarrayar Najeriya, shugaban kasar Muhammad Buhari ya kaddamar da wata sabuwar dabarar tunkarar rashin tsaron kasar.

Sabon salon tabbatar da tsaro na jami'an tsaron Najeriya

Sabon salon tabbatar da tsaro na jami'an tsaron Najeriya

Duk da cewar dai batun tsaron na zaman daya a cikin muhimman alkawura guda uku, da ke tsakanin gwamnatin tarrayar Najeriya da al'ummar kasar, an share shekaru hudu na farkon gwamnatin cikin hali na ha'ula'i.

Kama daga sake ta'azarar annoba ta ta'addanci ya zuwa rikicin makiyaya da manoma, sannan kuma da sabuwar dabarar satar al'umma, to dai an kare shekaru hudun gwamnatin sauyi, a cikin halin ba dadi.
Sai dai kuma da safiyar yau din nan gwamnatin kasar ta kaddamar da wani sabon shirin da ya kalli sauya dabarar tsaron, daga tabbatar da tsaron daukacin kasar ya zuwa mai da hankali ga tsaron dukiya da rayuwar al'ummar kasar.

Dabarar ta shekaru biyar dai za ta kalli inganta rayuwar al'umma, da rage fatara dama ilimi cikin kasar sannan, kuma da kai karshen al'adu irin na bara, da nufin tabbatar da komai dai dai a fadar janar Babagana Mungono da ke zaman mashawarci na tsaron kasar, da kuma ya jagoranci sabuwar dabarar da 'yan mulkin ke fatan za ta kai ga sauyin lamura.

Babagana Monguno mai bada shawara kan tsaro a Najeriya

Babagana Monguno mai bada shawara kan tsaro a Najeriya

“Mafitar tabbatar da zaman lafiya da ci gaba ita ce tabbatar da tsaro, da tsaro na tattalin arziki, da zamantakewar kowa. Abun da sabuwar dabarar ta yi shi ne hada batun tsaron al'adarmu da burin wannan gwamnati na yakar hanci, da samar da damar ilimi da kuma lafiya sannan kuma da ingantar noma.

Duk da cewar ba dole  bane ido ya kalli ainihin matsalolin da ke kasa, akwai wasu alamun da ke iya jawo muhimman matsaloli a tsakanin al'ummarmu. Dole ne in muna son kai karshen matsalolin rashin tsaro to sai mun kare matasanmu da ke ta karuwa, haka sai mun yakin jahilci da fatara. Batun rashin ilimi kuma na hade da rashin zuwan yara makaranta. Wannan batu na almijirci ba zamu iya cigaba da kau da ido a kansa ba. In kuma mun yi haka to kuwa zai juyo mana ta babbar hanya a nan gaba”

To sai dai koma ta ina 'yan mulkin na Abuja ke shirin su bi, domin tunkarar annobar ta tsaro dai, shi kansa shugaban kasar da ya kaddamar da dabarar ya ce gwamnatin kasar, ta kara a bisa tsofaffin muhimman batutuwa guda uku, na tsaro da tattalin arziki, da yakar cin hanci da ke gaba na gwamnatin can baya da kuma karawa tare da bunkasar noma da lafiya dama samun ilimi.

Nigeria Militärpolizei in Gwagwalada

Tankar yaki na jami'an tsaron Najeriya

“Ko bayan batun tsaro da tattalin arziki da yakar hancin da ke zaman muhimman batutuwan da muka sa a gaba a zangon farko na gwamnati, a zango na biyu mun kara tare da kallon ingantar ilimi da lafiya da harkar noma. Wannan sabbabi na dabaru na da babban burin tabbatar da ingantar tsaro a tsakanin al'umma.Duk da cewar tarrayar Najeriyar na kallon kanta, a zaman kasuwa mafi girma a nahiyar Africa, batun rashin tsaron da ake tahalla'kawa da rashin ilimin dai ya jefa tarnaki ga kokarin ci gaban al'umma.
To sai dai kuma dabarar da ke zaman ta bangaren zartarwa na da goyon bangaren majalisun dokoki na kasar, da ke fadin sun shirya tsaf, da nufin yin dokar hana bara, a cikin kasar a nan gaba.

“Akwai dai fatan nasara na wannan sabuwar dabara, wanda na iya kaiwa ga dorin dan ba a kokari na ingantar tattalin arziki, dama kila dora kasar a cikin jerin manyan kasashen duniya, a shirin da ke zaman mafi karfi na tattalin arziki a lokaci kankani.

Sauti da bidiyo akan labarin