1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
Lafiya

Saukaka hanyar zuwa a asibiti

September 6, 2017

A yunkurin taimakon mata masu juna biyu da ke zaune a yankunan karkara na Kenya wata kungiya ta samar da baburan masu kafa uku a matsayin motar daukar wadanda ke kan nakuda zuwa asibiti cikin gaggawa.

https://p.dw.com/p/2jQgG
Ebola Krankenhaus in Liberia
Hoto: Getty Images/J. Moore

Kungiyar wadda ta kasa da kasa ce ta ce ta yi hakan ne don ganin matan sun haihu lafiya kana abinda aka haifa bai fuskanci hadari ba yayin haihuwa.

Amfani da babura masu kafa uku don yin jigila ta fasinja a kasar Kenya ba sabon abu bana, sai dai a wannan karo wata kungiya mai zaman kanta da ke aiki wajen kyautata lafiyar mata musamman masu juna biyu wato Women and Health Alliance ko WAHA a takaice ta bijiro da sabuwar hanya ta amfani da irin wannan babura a yankin Mombassa da ke gabar ruwa inda aka maidasu motoci na daukar marasa lafiya musamman ma mata masu ciki. Kungiyar dai ta sanya kayayyaki da ake bukata wajen bada agaji ga marasa lafiya da kuma wanda ke kan gwiwa. Mariam Bashora guda ce daga cikin wanda suka amfana da wannan tsari kuma ta yaba.

Ita ma dai Mwantumu Bwanamkuu wadda ta amfana da wannan tsari na amfani da babur mai kafa uku wajen jigilar marasa lafiya ta ce shirin kyakkyawa ne duba da irin yadda ya ke taimakawa wajen rage wahalhalu na isa abiti ga masu juna biyu musamman ma dai mazauna yankunan karkara kuma hakan ya rage yawan matan da ke haihuwa a gidajensu maimakon asibiti.

Yanzu haka dai mata masu juna biyu da wadanda ke da yara kanana na ta rubibin cin gajiyar wannan shiri, batun da ya sanya bukatar da ake da ita ta wadannan babura na daukar marasa lafiya ta karu matuka. Wannan dai yanzu haka ya sanya mata da dama a Kenya yin kira ga wannan kungiya da ta kara yawan baburan don kaiwa ga sauran lunguna da sakuna na Mombassa da nufin agazawa masu karamin karfi wanda ba su da sarari fita daga karkararsu don zuwa asibiti.