Saudiyya za ta yi yaki da tsattsaurar akidar addini | BATUTUWA | DW | 25.10.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

BATUTUWA

Saudiyya za ta yi yaki da tsattsaurar akidar addini

Yarima mai jiran gado na kasar Saudiya, Muhammad Bin Salman, ya sha alwashin kawar da abin da ya kira, akidar matsanancin ra’ayin Islama da kasarsa ta jima ta na runguma.

Yarima mai jiran gado na kasar Saudiya, Muhammad Bin Salman, ya sha alwashin kawar da abin da ya kira, akidar matsanancin ra’ayin Islama da kasarsa ta jima ta na runguma, wacce kuma ake dangantawa da take kyankyasar da ‘yan ta’adda a duniya.

Hakan dai na zuwa ne ‘yan kwanaki bayan kame fitattaun Maluman da suka saba sukar Masarautar kan sauye sauyen da ta fara yi a bangaren addini.

Yarima mai jiran gado Muhammad Bin Salman, dan shekaru 32, wanda ake yi wa kirari da limamin sauyi, ya gargadi maluman da ke kokarin yi wa shirinsa kafar ungulu da su kuka da kansu:

“Yace mun kama hanyar komawa kan Addinin musulunci matsakaici, wanda ke koyar da riko da jimirin zama tare da ko wadanne akidu da addinai. Saba’in cikin dari na al’ummar Saudiya matasa ne ‘yan kasa da shekaru talatin, don haka, mu a zamaninmu, ba zamu bawa Maluma masu ra’ayin rikau da ke yada matsanancin ra’ayi dama ba”.

Wannan dai shine suka mafi muni da Yariman yayi karara ga Maluman masu ra’ayin rikau wadanda tuni aka tsare gwammansu, wadanda kuma suke da fada aji a mulkin kasar,

Yariman ya musanta zargin da wasu ke yi cewa, akidar wahabiyya da Salafiyya da kasar ke bi ce ta sanya su zama makyankyasar tarzoma da ta’addanci:

Masu fashin baki dai na ci gaba da dasa ayar tambaya kan cewa, ko yaya Masarautar ta Saudiya za tai da miliyoyin mutanan da ta dasawa irin wadannan akidar dake watse a sasssa daban daban na duniya?

 

 

Sauti da bidiyo akan labarin