1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Saudiyya: Tsagaita wuta a yakin Yemen

Binta Aliyu Zurmi
April 24, 2020

Kasar Saudiya ta sanar da tsawaita tsagaita wuta na tsawon wata guda a yakin da ta ke jagoranta a kasar Yemen bayan da wa'adin da ta dauka a baya ya kare a jiya Alhamis.

https://p.dw.com/p/3bMTF
Jemen Corona-Pandemie | Luftschlag auf Sanaa
Hoto: picture-alliance/Photoshot/M. Mohammed

Kamfanin dillancin labaran Saudiyya SPA ya rawaito mai magana da yawun dakarun hadin gwiwa Turki al-Malili na cewar an tsawaita wa'adin ne bisa bukatar manzon musamman na Majalisar Dinkin Duniya Martin Griffiths, domin samun damar ci gaba da tattaunawa.

Har wa yau daukar wannan mataki na da nasaba da kokarin da ake yi na ganin an dakile yaduwar cutar Corona a wannan wata na azumin Ramadana.