Saudiyya ta yi sassauci a batun man fetir | Labarai | DW | 28.09.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Saudiyya ta yi sassauci a batun man fetir

Iran dai ta tsaya kan bakanta cewa ba za ta sassauta ba kan danyen man da take fitarwa zuwa kasuwar duniya, saboda a cewarta ba ta dade ba aka janye mata takunkumin EU.

Saudi Arabien Dhahran Öl-Raffinerie (picture-alliance/dpa)

Faduwar farashin mai da Saudiyya ke fitarwa ya sa kasar cikin tasku

Nan gaba a cikin wannan shekara Kungiyar OPEC ta kasashe da ke fitar da albarkatun man fetir zuwa kasuwannin duniya za ta amince da ka'idar abin da kowace kasa mamba za ta fitar, abin da ke zuwa daidai lokacin da kasar Saudiyya mai fada a ji a kungiyar ta yi sassauci kan wasu kasashe da suka hadar da Iran da ke zama babbar abokiyar gaba a gareta.

Ministan makamashi a Saudiyya Khalid al-Falih ya bayyana a ranar Talata cewa Iran da Najeriya da Libiya ba su dama su fitar da abin da suke fitarwa zuwa kasuwa har mataki na karshe abu ne da za a ce akwai tsinkaye a cikinsa. Wannan dai ya nuna sauya matsaya daga bangaren na mahukuntan na Riyadh da suka nuna cewa ba za su rage abin da suke fitarwa kasuwa ba har sai dukkanin kasashen na OPEC da ma wanda ba mambobi na kungiyar ba sun bi layi, matakin da Iran ta daga yatsa cewa kada a taka mata birki ganin ba ta dade ba da aka janye takunkumin karya tattalin arziki da Kungiyar EU ta sanya mata ba.