1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Saudiyya ta tsare mata masu fafutukar 'yanci

Ramatu Garba Baba
May 22, 2018

An kama wasu mata bakwai masu fafutukar kare 'yancin mata a kasar ta Saudiyya bayan da aka zargesu da sukar manufofin gwamnati da kuma yunkurin kafa wata kungiya mai zaman kanta don yakar cin zarafin mata.

https://p.dw.com/p/2y8EJ
Saudi Arabien Verschleierte Frau in einem Auto in Riad
Hoto: picture-alliance/dpa/EPA/Str

Matan sun nemi kafa kungiyar da suka sakawa suna Amina, inda kungiyar za ta mayar da hankali kan duba irin cin zarafin da ake ko aka yi wa mata. amman gwamnatin Saudiyya ba ta kai ga amsa bukatar kafa wannan kungiyar ba.

Matan masu shekaru a tsakanin ashirin zuwa saba'in sun dadde suna fafutuka ta ganin an dage dokar hana mata tukin mota da kuma neman a basu 'yanci daidai dana yan'uwansu maza. Nan ba da jimawa ba ake sa ran gwamnatin Saudiyyar za ta janye dokar inda mata za su sami damar tuka kansu da kansu a cikin kasar.