1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Zargin Yarima Salman da kisan Khashoggi

Lateefa Mustapha Ja'afar
June 20, 2019

Mahukuntan Saudiyya sun yi fatali da rahoton binciken da Majalisar Dinkin Duniya ta gudanar dangane da kisan Jamal Khashoggi.

https://p.dw.com/p/3KlEO
Istanbul Agnes Callamard Sonderberichterstatterin willkürliche Hinrichtungen
Jami'ar Majalisar Dinkin DuniyaHoto: picture-alliance/AP/C. Yurttas

Rahoton dai ya yi zargin cewa akwai hannun Yarima Mohammed bin Salman a kisan fitaccen dan jaridar da ke sukan masarautar Saudiyya. Mahukuntan Riyadh sun nunar da cewa rahoton na kunshe da kura-kurai da rashin son gaskiya. Wata jami'ar Majalisar Dinkin Duniyar Agnès Callamard ce dai ta gabatar da rahoton binciken, inda ta nunar karara cewa akwai bukatar a tuhumi yarima mai jiran gado na Saudiyyan Mohammed bin Salman dangane da kisan gillar da aka yi wa Khashoggi a karamin ofishin jakadancin Saudiyan da ke birnin Santanbul na Turkiyya, tana mai cewa akwai alamu da ke nuna Yarima bin Salman na da hannu dumu-dumu a kisan.