Saudiyya ta kafa rundunar yaki da ta′addanci | Labarai | DW | 15.12.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Saudiyya ta kafa rundunar yaki da ta'addanci

A wani mataki na yakar ta'addanci da ke addabar duniya musamman yankin Gabas ta Tsakiya, kasar Saudiya ta kafa rundunar hadin gwiwa ta kasashen Musulmi 34.

Kasar ta Saudiyya ta kafa wannan runduna ta musamman ne tare da wasu kasashen Musulmi da za ta dukufa kan yaki da ta'addanci. Wannan runduna dai ta hada kasashen 34 cikinsu har da kasashen Masar, Pakistan, da Senegal. Sai dai wannan runduna an kafa ta ne ba tare da kasar Iran ba, kuma Saudiyya ce za ta jagorance ta, inda aka kafa cibiyar rundunar a birnin Ryad na kasar ta Saudiyya.