Saudiyya: Mata za su fara samun sakon saki ta salula | Zamantakewa | DW | 08.01.2019
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Zamantakewa

Saudiyya: Mata za su fara samun sakon saki ta salula

A Saudiya,wata sabuwar dokar kasar da za ta bai wa mata damar sanin mazajensu sun sakesu, tun kafin su sanarwa alwalinsu ko iyaye da muharammansu na ci gaba da jawo cece-kuce a kasar.

Daga ranar Lahadin da ta gabata, kotunan kasar za su bukaci mazan aure su aika wa matansu shaidar saki ta hanyar sakon wayar salula, ba tare da sanarwa alwaliyen matan ba, kamar yadda ake yi a da, batun da wasu ke yi wa kallon ci gaba ne na irin 'yanci da sakin mara ga matan kasar ta Saudiya da yarima mai jiran gadon kasar Muhammad Bin Salman ya faro. Mahukuntan na Saudiyya dai sun sha nuna cewar matan kasar sun jima suna shigar da kara a kotunan kasar kan mazajensu da ke sakinsu ba tare da saninsu ba.

Sauti da bidiyo akan labarin