1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Zanga-zangar adawa da tsare Falisdinawa

Ramatu Garba Baba
October 16, 2019

Falisdinawa sun gudanar da zanga-zangar adawa da samamen da Saudiyya ta kai kan al'ummarta a sassan kasar inda ta kama mutane da dama da suka ce ana gallaza wa ukuba.

https://p.dw.com/p/3RO1Z
Palästina Tod eines Gefangenen Rückkehr der Leiche nach Hebron
Hoto: Hazem Bader/AFP/Getty Images

Iyalan fursinonin sun gudanar da zanga-zangar a harabar wani ofishin kungiyar agaji ta Red Cross a birnin Gaza, sun yi kira da a daina gallaza wa fursunonin bisa zargin hannu a ayyukan ta'addanci. Amma kakakin kungiyar ta Hamas ya musanta wadannan zarge-zargen inda ya ce matakin kai samamen da Saudiyya ta yi inda ta kame Falisdinawa fiye da hamsin ciki har da likitoci da manyan 'yan kasuwa, ya biyo bayan sulhun da kungiyar ta yi ne da gwamnatin Iran da yanzu haka ke takun saka da Saudiyyan. An gano yadda fursunoni ke cikin wani yanayi da aka ce ya tauye 'yancin kowanne dan Adam.