1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Fararen hula na kara hallaka a Yemen

Lateefa Mustapha Ja'afar
September 2, 2019

Kungiyar agajin ta duniya wato Red Cross ta ce harin rundunar taron dangi da Saudiyya ke wa jagoranci a Yemen, ya sauka a wani waje da 'yan tawayen Houthi ke tsare masu laifi.

https://p.dw.com/p/3Os4M
Luftangriffe im Jemen
Sabon harin Saudiyya da kawayenta ya hallaka fararen hulaHoto: picture-alliance/dpa/AP/H. Mohammed

Shugaban tawagarta Red Cross a  Yemen Franz Rauchenstein ya bayyana harin da cewa abin damuwa ne matuka, yadda gawarwakin mutanen ke warawatse a karkashin barakuzan gine-gine, inda ya ce babu abin da mutum zai iya bayyana harin da shi illa bakin ciki da takaici. Rauchenstein ya kara da cewa, kawo yanzu ba su da tabbacin adadin wadanda suka hallaka a wajen da ake tsare da kimanin mutane 170. Shi ma a nasa bangaren, jakadan musamman na Majaalisar Dinkin Duniya a Yemen din Martin Griffiths ya bayana harin da wani babban abin tashin hankali da takaici, yana mai cewa rayukan al'ummar Yemen da ake rasawa a yakin sun yawaita kuma tilas a kawo karshen hakan. Tun dai a shekara ta 2015 ne rundunar taron dangin karkashin jagorancin Saudiyya ta fara kai hare-hare a Yemen din, a wani mataki da Saudiyyan da kawayenta suka bayyana da kokarin kare halastacciyar gwamnati da al'ummomin kasa da kasa suka amince da ita a kasar, hare-haren kuma da kawo yanzu suka lakume dubban rayuka.