Saudiya: An kori wasu kusoshin gwamnati | Labarai | DW | 05.11.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Saudiya: An kori wasu kusoshin gwamnati

Yerima mai jiran gado a kasar Saudiyya Mohammed bin Salman, ya sallami wasu masu fada a ji a gwamnati tare da tsare wasu yerimomi 11 da wasu tsoffin ministoci da ake zargi da handame dukiyar kasa.

Yerima Alwaleed bin Talal da ke zama shahararren mai kudi da ke zuba jari a kasar ta saudiyya na cikin wadan da aka tsare, an kuma kori dan marigayi sarki Abdalla Yerima Miteb bin Abdullah, inda aka maye gurbinsa da Khaled bin Ayyaf.

Wannan mataki na korar wasu jami'an gwamnati tare da yin karambawul a wasu ma'aikatun kasar ta Saudiyya, na zuwa ne jim kadan bayan da yerima bin Salman ya fara jagorantar wani sabon kwamiti da mahaifinshi ya nada, da nufin gudanar da bincike kan ayyukan cin hanci da rashawa tare da farfado da tattalin arzikin kasar, ta yadda za a ci gaba da jan hankalin masu zuba jari daga sauran kasashen duniya.

Gwamnatin Saudiyya ta ce wannan sabon kwamiti na da karfin tuhumar duk wani jami'n gwamnati na yanzu ko na baya da ake zargi da aikata ba dai dai ba, wannan mataki dai ana gani tamkar share fage ne da sarkin Saudiyyan ke yi na sauka daga karagar mulki domin bawa dansa damar rike masaurautar.