Sauƙaƙa wayar salula a ƙasashen EU | Labarai | DW | 11.09.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Sauƙaƙa wayar salula a ƙasashen EU

Wani daftarin ƙungiyar Tarayyar Turai, zai cire ƙarin cajin kuɗin buga wayar salula in mutun ya tsallaka wata kasar da ba inda ya yi rijistar wayar ba.

#34725576 - Gruppe mit Handys im Restaurant © Robert Kneschke

Wasu 'yan Turai ke amfani da salula yayin hutawa

Ƙungiyar Tarayyar Turai na tsara wani shiri da zai bai wa masu amfani da wayar salula a stakanin ƙasashen ƙungiyar 28, damar buga waya a ko wace ƙasa tamkar suna ƙasashensu na asali, wato babu ƙarin kuɗi, wanda ake ƙira Roaming a turance. Wani daftarin da majalisar dokokin ƙungiyar EU ta fitar, ya ce idan aka samar da shirin, to a duk ƙasashen EU 28 za ka buga waya tamkar a gidan ka. Wannan tsarin wata babbar han'ya ce ta sauƙaƙa buga wayar tafi da gidanka a ƙasashen na Tarayyar Turai, inda kusan kowa ya mallaki wayar salula. Ministan sadarwa a hukumar EU Neelie Kroes ta ce manufar shirin ita ce bai wa 'yan ƙasashen mambobin ƙungiyar damar cin moriyar buga waya, ba tare da ƙarin wani cajin kuɗi ba, ta yadda ba za a yi la'akari da ga ƙasar da mutun yake ba.

Mawallafi: Usman Shehu Usman

Edita: Mohammed Nasir Awal