Satar mai na sa Najeriya asarar miliyoyi | Zamantakewa | DW | 09.01.2019
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Zamantakewa

Satar mai na sa Najeriya asarar miliyoyi

Majalisar Dinkin Duniya ta ce Najeriya ta yi asarar kudin shiga da ya kai kusan dala miliyan dubu uku sakamakon aikin masu satar danyen mai a yankin Niger Delta.

Brennende Ölpipeline in Nigeria

Ofishin Majalisar Dinkin Duniya a shiyyar Afirka ta Yamma wanda ya fitar da wannan bayanin ya ce dalar Amirka biliyan dubu biyu da miliyan dari takwas Najeriyar ta rasa a dalilin sace-sacen da ake yi na danyen manta wanda kuma ake sayar da shi a ciki da wajen kasar.

Wannan hasarar dai a cewar Majalisar ta Dinkin Duniya, ta afku ne a tsakanin 1 ga watan Yuli na shekarar 2018 zuwa 31 ga watan Disamba na 2018, wato cikin watanni shida kacal.

Nigeria Rebellengruppen legen Waffen nieder

Wasu 'yan tsagerun Niger Delta

Majalisar Dinkin Duniyar ta kara da cewar, ta’asar barayi a gabar tekun Guinea, lamari ne da ya tsananta a tsakankanin watan Janairu zuwa watan Nuwamba na shekarar 2018, inda ta ce ‘yan fashin sun kai farmaki kan jiragen ruwa na kasa da kasa har kimanin sau 82.

Masu irin wannan ta’annati ga danyen man na Najeriya kan haifar da mummunar tsiyayar mai da kan malale kasa da teku da kuma gonakin mazauna yankin da ake hakar man wanda kuma hakan, kan haifar da gurbatar muhalli da ke kassarar rayuwar al'ummomi da dama a yankin na Niger Delta. Tsiyayar danyan mai na daga cikin dalilai da ke rura wutar tada kayar baya a yankin mai arzikin mai.

Sauti da bidiyo akan labarin