Sassauta dokar yawo da makami a Isra′ila | Labarai | DW | 18.11.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Sassauta dokar yawo da makami a Isra'ila

Mahukuntan Isra'ila sun ce za su sassauta dokar nan ta amfani da makamai a wani mataki na baiwa jama'a dama ta kare kansu daga dukannin wata barazana da ka iya taso musu.

Ministan tsaron al'umma na kasar Yitzhak Aharonovitch ya ce gaba kadan a yau ne suke son aiwatar da wannan tsari sai dai zai shafi wanda ke da lasisi na mallakar bindiga ne kawai gami da sojojin da ba sa kan aiki da kuma irin jami'an tsaron nan wanda ba na hukuma ba.

Wannan dai na zuwa ne bayan da wasu Falasdinawa suka hallaka wasu mutane hudu tare da raunata karin wasu a wani farmaki da suka kai wajen ibadar Yahudawa a birnin Jerusalam, harin da mahukuntan Falasdinu suka yi Allah wadai da shi.