1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

060608 Dialog Kosovo

Slavkovic, Filip August 28, 2008

Tun kimanin shekaru 600 da suka gabata musulunci ya yaɗu a matsayin wani addini na masu sassaucin ra´ayi a ƙasashen kudu maso gabashin nahiyar Turai.

https://p.dw.com/p/F6Pd
´Yan rawar Sota ta al´adun gargajiyar al´umar KosovoHoto: Refki Alija

Jama´a masu sauraro barkanku da warhaka, barkanmu kuma da saduwa da ku a cikin wani sabon shirin na Taɓa Ka Lashe, shirin da ke duba batutuwan da suka shafi addinai, al´adu da zamantakewa tsakanin al´ummomi daban daban a wannan duniya ta mu.

A cikin shekaru kusa takwas da suka wuce a nan Turai an fi yiwa addinin musulunci kallon wani addini na ´yan tarzoma da masu tsauttsauran ra´ayi musamman malaman masallatai na irin unguwannin wajen garin a manyan biranen ƙasashen yamma. To sai dai abin da ake manta da shi shi ne tun kimanin shekaru 600 da suka gabata musulunci ya yaɗu a matsayin wani addini na masu sassaucin ra´ayi a ƙasashen kudu maso gabashin nahiyar Turai. A cikin shirin na yau za mu duba yadda addinin ya yaɗu ne a Kosovo ƙasar dake zama jaririya mai rinjayen musulmi a duniya.

Tun a cikin ƙarni na 14 addinin musulunci ya bazu a yankin Balkan sakamakon daular Othmaniya da ta wanzu tsawon shekaru 500. Ko da yake a wancan zamani Turkawan ba su tilastawa waɗanda ba musulmi ba su musulunta, amma da yawa daga cikin Kiristoci a yanki sun karɓi addinin na musulunci. Domin a wancan lokaci zama musulmi daidai yake da samun cikakkiyar karɓuwa a cikin jama´a tare da samun wata gata ta daban tsakanin shugabannin musulmin idan aka kwatanta da tsakanin shugabannin Kiristoci. Ɗaukaci kuwa al´umar yankin Bosniya da kuma Albaniyawa suka fi musulunta. Bayan rugujewar daular Othmaniya wata gamaiyar Islama ta zauna da gindinta a yankin da a yanzu ya zama Kosovo.

To sai dai an miƙawa Sabiyawa mabiya ɗarikar Orthodox ragamar wannan yanki bayan kafa wata ƙasa a yankin Balkan. Tun a wancan lokaci sama da kashi 50 cikin 100 na mazauna wannan yanki Albaniyawa ne da kuma Musulmi. Ga babban malamin addinin musulunci Qemajil Morina wannan tamkar faɗuwa ce ta zo daidai da zama.

1. „Mun tashi ne a cikin wata al´uma mai ƙabilu da kuma mabiya addinai daban daban. Muna girmama haka. Na yi karatun jami´a a Sudan da Masar na kuma na taɓa zama a Libya. Yadda suke tafiyar da addinin a can ya ɗan banbanta da a nan. Mu a nan mun fahimci cewa Sabiyawa na da ´yancin zuwa coci don tafiyar da addininsu. Haka nan ma ´yan Katholika. Mun amince da waɗanda ba sa bin kowane addini domin a zamanin mulkin kwaminisanci al´umar Albaniyawa ba ruwansu da addini.”

Gwamnatin kwaminisanci musamman ta maƙwabciyar janhuriyar Albaniya ta kasance gwamnatin kama karya. Tun a ƙarshen shekarun 1980 Albaniyawan Kosovo sun yi ta fafatawa da wata gwamnatin masu ra´ayin kishin ƙasa ta Sabiya. Kuma tun a 1998 ´yan kishin Albaniya suka yi ta fafatukar nemawa yankin Kosovo ´yanci yayin da ita kuma Sabiya ta yi ta ɗaukan matakan ba sani ba sabo na lalata tanade-tanaden ci-gaban yankin musamman ma masallatai inda aka rushe da dama. Farfesa na Islama Qemail Morina ya ce a lokacin yaƙin al´umar yankin sun fi ma rungumar addinin.

2. “Yanzu haka muna da matasa da ke aiki da dokokin addinin. Musmaman a lokacin sallar Juma´a ba tsofaffi ne kaɗai ake gani a cikin masallatai ba kamar yadda ya kasance a zamanin mulkin kwaminisanci. To sai dai matasan ba sa azamar zuwa sallar Juma´a. Yawan su ba ya haura kashi 10 cikin 100 musamman a bukukuan idi.”

To sai dai duk da haka a kullum sashen addinin Islama na jami´ar Kosvo a cike ya ke da ɗalibai. Adem Morina daga garin Prizren dake yankin kudancin Kosovo ya yi bayani dangane da dalilan da suka sa shi neman ƙarin ilimin addinin.

3. “Muna zaman lafiya da girmama juna a garin Prizren. Ko da yake a al´adun mu a Prizren sun ta´allaka da addinin musulunci amma akwai kyakkyawan zaman cuɗe-ni in cuɗe-ka tsakanin Sabiyawa da Turkawa da kuma Bosniyawa. Na shiga wannan sashen ne domin ba da ta wa gudunmawa ga matasan garin mu, musamman game da addinin musulunci.”

Ba dukkan Albaniyawa ne musulmi ba. A Kosovo alal misali kashi 4 cikin 100 mabiya ɗarikar Katholika ne. Sannan da yawa daga cikin musulmin kuma ´yan tsirarun ƙabilu ne kamar Turkawa, Bosniyawa da kuma ´yan Roma. Yanzu haka dai akwai masallatai kimanin 650 a Kosovo. Ko da yake yanzu haka ana ci-gaba da gina sabbi amma ba da sauri ko da yawa kamar a Bosniya ba.

Dangane da ƙwace kadarorinsu a zamanin mulkin kwaminisanci gamaiyar musulmi a Kosovo ba su da ƙarfin tattalin arziki. A halin da ake ciki kaɗan ne daga cikin musulmin ke ba da karo-karo na euro biyu a wata ga gamaiyar su. Musulmin na Kosovo dai suna ɗari-ɗari da karɓar taimako daga ƙasashe masu arzikin man fetir inda ake bin tsauraran dokokin addinin, inji Farfesa Qemajil Morina.

4. “Ba mu da wata matsala da Wahabiyawa. A lokacin da ƙungiyoyin agaji na farko daga Saudiyya da sauran ƙasashen Gabas Ta Tsakiya suka zo, mun nuna musu a fili cewa dole ne taimakon da za su bayar ya zama na jin ƙai kaɗai, kuma ba su da wani iko na yaɗa ra´ayoyinsu ko koyar da addinin musulunci a nan.”

Morina yana alfahari da sassaucin ra´ayin addinin musulunci da Albaniyawa da Bosniyawan yankin Balkan ke bi. Ya ce hakan ka iya zama abin koyi ga sauran musulmi a Turai baki ɗaya. A halin da ake ciki wakilan musulmin Albaniyawa sun wani ɓangare a tattaunawa tsakanin addinai daban daban a nahiyar Turai.

To sai dai a Kosovo ana fuskantar matsala a dangantaka da majami´ar Orthodox bisa dalila da dama da suka haɗa har da murƙushe ´yan fafatukar neman ´yanci da Sabiya ta yi a cikin shekarun 1990 sai kuma matakan ba sani ba sabo da Albaniyawa suka ɗauka kan Sabiyawa a shekarun farko na wannan ƙarni. Ko da yake an yunƙuro don tuntuɓar juna a wannan fanni amma ganin laifin juna da suke yi ya sa har yanzu ba a cimma tudun dafawa ba.

Ra´ayin masu lura da al´amuran yau da kullum ya zo ɗaya cewa rikicin Kosovo tsakanin Sabiyawa da Albaniyawa ba na addini ba ne, rikici da ke da nasaba da siyasa da kuma ƙabilanci. Su ma al´umar Albaniyawa sun sha jaddada haka inda suka yi imani da al´adun su na gargajiya da ke fifita namiji kan mace fiye da wasu dokoki na addini. Farfesa Morina yayi korafi kan haka yana mai cewa.

5. “Dole ne mu nunawa duniya matsayinmu da abin da muka yi imani kansa. Munafunci ne mu riƙa yi wasu abubuwa tamkar mu ba musulmi ne ba. Haƙiƙa addinin musulunci ya zauna da gindinsa a cikin mu. Shi ya sa kuskure ne idan wannan al´uma ta nesanta kan ta daga addinin. Muna fargabar cewa ana iya danganta matsalarmu da addinin musulunci.”

Wannan matsala dia ita ce ta neman ´yancin kai. Kafin su samu wannan ´yanci daga Sabiya sai da Albaniyawan Kosovo suka bukaci goyon baya daga kasashen yamma.

6. „Har yanzu ana matukar sha´awar addinin musulunci a yankin da na fito. Mutane na kara yin imani da wannan addini. Ko da yake a nan sun fi mu yawan mutane amma basa sha´awar addinin kamar a wurin mu.“