Sasantawa game yunƙurin juyin mulkin Madagascar | Labarai | DW | 18.11.2010
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Sasantawa game yunƙurin juyin mulkin Madagascar

Gwamantin Madagascar ta fara duba yiwuwar yi wa bijirarun sojojin da suka yi yunƙurin juyin mulki afuwa.

default

Shugaba Andry Rajoelina na Madagascar kewaye da sojoji

Hukumomin Madagascar sun yi alƙawarin yi wa bijarun sojojin da suka yi yunƙurin juyin mulki afuwa matiƙar suka ci gaba da biyeyya ga shugaba Andry rajolina da ke ci a yanzu. Wata majiyar rundunar sojojin ƙasar ce ta bayyana wa kanfanin dillancin labaran Faransa wato AFP cewar, hukumomin Madagascar sun fara tattaunawa da bijirarrun sojojin domin nazarin hanyoyin da za a bi wajen kauce ma gurfanar da su gaban ƙuliya bisa zargin laifin cin amanar ƙasa.

Gungun sojojin da yunƙurinsu na kifar da gwamanti ya ci tura na ci gaba da samun mafaka a wani barikin sojen da ke kusa da babban filin jirgin saman birnin Antananarivo. Su dai hapsoshin sojen da yawansu ya zarta 20, sun yi da'awar ƙwace mulki ne a jiya a daidai lokacin da ake gudanar da zaɓen raba gardama da al'umar ƙasar suka amince da shi da gagrumin rinjaye. Shugaban da ke ci a yanzu wato Andry Rajilina ya ƙaryata iƙirarrin kifar da gwamantinsa.

Mawallafi: Mouhamadou Awal

Edita: Halimatu Abbas