Sarrafa nau′o′i daban-daban na shara a Kano | Himma dai Matasa | DW | 13.01.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Himma dai Matasa

Sarrafa nau'o'i daban-daban na shara a Kano

Gambo Dan Daru injiniya ne da ya kware wajen hada manyan injuna da suke sharrafa shara, kuma ya yi fice wajen sayar wa masana'antu da ke bukata kayan Bola.

A halin yanzu ya kware wajen tayar da tsofaffin injunan sarrafa kayan masana'antu wadanda ya kan sayo daga wasu kasashen Africa. Yana horas da matasa dabarun dogaro da kai ta hanyar samo masa kayan sarrafawa a masana'antarsa a kauyuka da kuma yadda yake wargaza irin wadannan manyan injuna ya tayar da wasu yana mai cewa.

"Abubuwa ne da yawa acikin tafiya. Ka zo ka same ni ma ina aikatawa. Ina hada Inji, ina sayar da raw materials injin din (Kayan gyaran injuna) kuma ina sayar da materials da injin yake sarrafawa."

A harabar masana’antar injuna ne manya da kanana yana cirar wasu bangarori na wasu injunan yana tayar da wasu, kuma ya yi bayani kan inda yake samo da kayayakin:

"Wadan su a kan same su daga jihohin nan namu na Nigeria kamar irin su Lagos da Onitsha, Wasu kuma sai mun haura wasu kasashe kamar irin su Cote D’Ivoire da Ghana da Jamhuriyar Demokaradiyyar kwango, Chadi ko Kenya. Na je Nijar kan harkar robobi. Wasu ba su da wayewa kan sarrafawar mashinan. Sai na je zan ba su gudunmowa, wasu kuma injunan za su sa a kasuwa saboda sun kasa fahimtar yadda za su sarrafa mashinan, mu kuma muna da basirar yadda muke yi da su sai mu je mu sayo mashinan mu kawo nan Nigeria mu hada mu ci gaba da aikin mu."

A cikin masana’antar kuwa ma’aikatansa ne suke ta sarrafa nau’o’i daban- daban na shara.

"Shi recycle kamar abin da ya danganci sharar leda, sharar roba, da sauran sharar matattun buhuna a yi a yi maida shi tabarma, wani kuma a yi robobi da su kuma kamar ledar pure water (ta ruwan sanyi) da ake tsinta ana sarrafa ta ne masu Kamfanonin yin takalman slipper din nan suna saye suna kara yin slippers din nan da ake ce musu toilet slippers na wanka."

Yanzu Alhaji Gambo Dan Daru yana da irin wannan masana’anta a wurare uku, Kano da Gombe da kuma wata sabuwa a Abuja. Malam muhiyyiddeen Tijjani yana daya daga cikin yaransa da ya horas wanda shi ma ya na alfahari ya koya wa wasu.

"Da ban iya komai ba, yanzu kuma injuna da yawa duk zan iya gyarawa da sauransu, kuma ni kai na a karkashina akwai yara ina kula da su a yanzu haka akwai injuna shida wadanda nasa ne crushing suke yi, ni na ke zuwa na gyara musu da. Wuri da yawa a Gombe akwai aikin da ake da yawa a can kuma a yanzu haka akwai injuna uku ana hada wa suma za'a kara turawa Abuja."

Alhaji Gambo Dan Daru ya ce yana da gudunmowa mai yawa da zai bayar a yanzu haka da zaran gwamnatin Tarayyar Nigeria ta fifita manufarta ta gina Dan Adam.

Sauti da bidiyo akan labarin