1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
Tattalin arziki

Sauyi kan hanyoyin sarrafa nama a Jamhuriyar Nijar

Salissou Boukari SB
May 29, 2019

Wata matashiya sa'adatu Sabi'u bayan kammala karatu na jami'a maimakon jiran aikin gwamnati ta rungumi sana'ar sarrafa nama inda take yin dambun nama a kokarin da ta sanya a gaba na tsayawa da kafarta a Jamhuriyar Nijar.

https://p.dw.com/p/3JTMY
Frankreich - Halal
Hoto: picture-alliance/maxppp/J. PELAEZ

Wata matashiya sa'adatu Sabi'u bayan kammala karatu na jami'a maimakon jiran aikin gwamnati ta rungumi sana'ar sarrafa nama inda take yin dambun nama a kokarin da ta sanya a gaba na tsayawa da kafarta.

Ita dai malama Sa'adatu na hada dambun naman da kayan hadi masu tsafta kana ta dauka ta zuba a leda da kwanso na kwali kai ka ce wani kamfani ya hada kayan.

Wannan matashiya ta kan sanya kayanta a shafukan sada zumunta ga misali a shafin Facebook idan masu son hajarta sun gani su kira su sayi kayan a kai masu har gida su biya kudin kayan da suka saya su ba da kudin motar kawowa.

Wannan sana'a dai ta Sa'adatu ba ta tsaya ga kanta ba har da koyar da wasu sana'ar da suke yi tare da alfahari da ita. Fatan Sa'adatu dai shi ne ta fadada kamfanin nata ya zamana tana kara samar da aiki ga matasa, inda ma take kalubalantar mata su tashi su rungumi sana'a don dogaro da kai.