1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sarkozy ya yi gargadin kai harin 'yan ta'adda

October 14, 2016

Tsohon shugaban kasar Faransa Nicholas Sarkozy ya yi amfani da muhawarar da aka watsa ta kafar talabijin a ranar Alhamis inda ya ce akwai fargabar yiwuwar kai sabbin hare-hare a kasar.

https://p.dw.com/p/2RD72
Frankreich Erste Fernsehdebatte zwischen den sieben Kandidaten
Hoto: Picture-Alliance/dpa/P. Wojazer

Tsohon shugaban ya ce ba magana ba ce ta idan za a kai hari ba, a a yau she ne za a kai shi, wannan ne abin tambaya.

Sarkozy ya bayyana haka ne a muhawara da suka yi da sauran 'yan siyasa shida da ke neman tsayawa jam'iyyar  'yan Conservative masu ra'ayin mazan jiya a zaben shugaban kasa a shekara mai zuwa.

Sarkozy da abokin karawarsa Alain Juppe sun maida hankali kan  batun yaki da ta'addanci a muhawarar inda Sarkozy ke neman a kai ga garkame wadanda ke zama babar barazana cikin wadanda ya kira "Masu tsatstsauran kishin addinin Islama". Juppe na kafewa a kan cewa alkali shi ke da tacewa.

Za dai a yi zaben fidda gwani na masu ra'ayin mazan jiya a ranakun 20 da 27 ga watan Nuwamba mai zuwa.