1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sarkin Spain zai mika wa dansa mulki

June 2, 2014

Sarkin Spain zai yi murabus bayan sarautar shekaru 40, yayin da Sarauniyar Ingila da ta shafe shekaru fiye da 60 babu alamu za ta muka mulki tana raye.

https://p.dw.com/p/1CAnI
Hoto: picture-alliance/dpa

Sarkin Spain Juan Carlos ya bada sanarwar cewa zai yi murabus inda zai mika mukamin wa dansa. Sarkin ya bayyan haka ne cikin wata sanarwar da aka yada a kasar a wannan Litinin.

Sarki Juan Carlos dan shekaru 76 da haihuwa yayi mulki na kusan shekaru 40, kuma ya taimakawa kasar wajen fitar da ita daga mulkin kama karya zuwa na Demokradiya, amma a bisa matsalolin da kasar ke fuskanta na bangaren tattalin arzikin zai sauka domin ya baiwa dansa Yarima Felipe mulkin kasar.

Sarki Carlos dai bai bayyana ranar da zai sauka ba domin sai gwamnatin kasar ta bayyana kudirinta dangane da nada dan sarkin Felipe mai shekaru 46 a matsayin sabon sarkin na Spain. Yanzu haka dai a nahiyar Turai sarauniyar Ingila Elizabeth ta biyu 'yar shekaru 88 da haihuwa ke kasancewa mafi dadewa a kan gadon sarauta, inda ta shafe fiye da shekaru 60 a kai.

Mawallafiya: Zainab Babbaji Katagum / Suleiman Babayo
Edita: Mohammad Nasiru Awal