Sarkin Qatar ya sauka daga mulki | Labarai | DW | 25.06.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Sarkin Qatar ya sauka daga mulki

Wannan shi ne karo na farko da wani sarki a yankin ƙasashen larabawa ya miƙa mulki kafin mutuwa.

Sarkin Daular Qatar Sheikh Hamad bin Khalifa Al Thani ya yi murabus tare da miƙa ragamar mulkin ƙasar ga ɗansa Shikh Tamim. Sarkin dai ya sanar da hakan ne a wani jawabi da ya yi ga al'ummar daular ta gidan talabijin inda ya buƙaci su da su bai wa sabon jagorandukkanin goyon bayan da ya kamata.

Tun a cikin shekara ta 2003 ne dai ta fito fili cewar Sarkin zai miƙa ragamar sauratar daular ga ɗan nasa wanda ake ganin mataki ne da ba kasafai sarakuna kan ɗauka ba. Qatar dai ƙarƙashin jagorancin Sheikh Hamad bin Khalifa Al Thani ta samu bunƙasa musamman ma dai ta ɓangaren tattalin ariziki da ma da ƙarfin faɗa a ji tsakanin takwarorinta.

Mawallafi : Abdourahamane Hassane

Edita : Saleh Umar Saleh