1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sarkin Malesiya ya yi murabus

Yusuf Bala Nayaya MNA
January 6, 2019

Sarki Sultan Muhammad na biyar na Malesiya mai babbar daraja a sarautar kasar ya yi murabus daga mukaminsa shekaru biyu kacal bayan da ya hau karagar mulki.

https://p.dw.com/p/3B5oy
Malaysia König Muhammad V.
Hoto: picture-alliance/dpa/F.Ismail

Fadar sarkin na Malesiya ta bayyana a wannan Lahadin cewa sarkin Sultan Muhammad na biyar mai shekaru 49 ya yi murabus ba tare da ba da dalili na saukar ba.

Wannan dai shi ne murabus na farko ga wani sarkin Malesiya mai wannan daraja a tarihi. Ya dai kasance jagora a jihar Kelantan da ke yankin Arewa maso Gabashi. Kafin murabus din nasa a wannan rana ta Lahadi, ya hau karagar mulki a watan Disamba shekarar 2016, inda ya zamo sarki da kankantar shekaru cikin masu rike da wannan sarauta da kundin tsarin mulki a Malesiya ya amince da su.

Karkashin tsari da ake bi tun bayan da Malesiya ta samu mulkin kanta daga Birtaniya a 1957, masarauta daga jihohi tara ke karba-karba ta wannan kujera tsawon wa'adi na shekaru biyar kowanne tsakaninsu.