Sarkin Belgium ya sauka daga sarauta | Labarai | DW | 21.07.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Sarkin Belgium ya sauka daga sarauta

A karo na farko a tarihin kasar Belgium, sarkin kasar Albert na biyu ya sauka daga gadon sarauta inda ya bawa dansa Philippe ragamar gidan sarautar.

Sarkin kasar Belgium Albert na biyu ya sauka daga kan gadon sarauta inda ya mikawa babban dansa Yarima Philippe ragamar sarautar a wani buki da aka gudanar a fadar sarkin dake Brussels babban birnin kasar.

Da yake jawabin sa na karshe yayin mika sarautar ga dan nasa a gidan talabijin din kasar, Albert ya bayyana cewa " Ina so in kammala mulkin sarautar kasar nan da yi wa sabon sarki fatan alkhairi, a matsayi na na sarki kuma baba a gareshi. Ina yi wa Yarima Philippe da Gimbiya Mathilde fatan alkhairi da kuma fatan zaku ba su goyon baya".

Wannan dai shine karo na farko da sarki ya sauka daga kan gadon sarauta domin radin kansa a kasar ta Belgium, wanda hakan ya baiwa Yarima Philippe na daya dake da kimanin shekaru 53 a duniya, damar zama sarki na bakwai a tarihin kasar.

Mai kimanin shekaru 79 a duniya sarki Albert na biyu ya sauka daga gadon sarautar ne sakamkon shekaru da kuma rashin isasshiyar lafiya wanda hakan ya kawo karshen shekaru 20 da ya kwashe ya na mulkar kasar.

A bisa al'ada dai gidan sarauitar na Belgium na taka muhimmiyar rawa a al'amuran tafiyar da mulki, in da sarki yake zaman shugaba kuma babban kwamandan askarawan kasar.

Mawallafiya: Lateefa Mustapha Ja'afar
Edita: Umaru Aliyu