1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sarkin Oman Qaboos ya rasu

Abdul-raheem Hassan
January 11, 2020

Allah ya yi wa Sarki Qaboos bin Said al Said na Oman rasuwa yana da shekaru 79 da haihuwa, kamin mutuwarsa shine sarki mafi dadewa a karagar mulkin sarauta da karfin fada a ji a yankin Gabas ta Tsakiya.

https://p.dw.com/p/3W1to
Oman Maskat | Tod von Sultan Kabus bin Said
Hoto: Reuters/AFP/A. Caballero-Reynolds

Ya fara mulki a shekarar 1970 bayan yiwa mahaifinsa juyin mulki shekaru 50 da suka gabata da niyyar kawo sauyin siyasa, sai dai 'yan fafutuka sun koka da da rashin samun 'yanci a mulkinsa.

Ba a bayyana dalilan mutuwar sarkin ba kawo yanzu, amma rahotanni na cewa marigayin ya shafe kusan mako guda yana jinya a kasar Beljiyam kamin mutuwarsa bayan fama da rashin lafiya na kusan shekara guda.

An ayyana zaman makoki na kwanaki uku, yayin da gidan talabijin na aljazeera ya ruzuwaito tuni aka nada Haitham bin Tariq al-Said a matsayin sabon sarkin Oman sakamakon rashin magajin da daga marigayi Sarki Qaboos.