1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaTurai

Sarki Charles na Burtaniya ya samu kyakkyawar tarba a Sydney

Abdulkarim Muhammad Abdulkarim
October 20, 2024

Wannan ce ziyararsa ta farko a kasar waje, tun bayan kamuwa da cutar kansa, kuma ta 16 a kasar Australia, wadda ya yi karatu a cikinta lokacin yana matashi a shekarar 1966

https://p.dw.com/p/4lzph
Sarki Charles na Burtaniya da Sarauniya Camilla
Hoto: Hannah McKay/REUTERS

Daruruwan mutane ne cikin murna suka tarbi Sarki Charles na Burtaniya da sarauniya Camilla a Lahadin nan a birnin Sydney na kasar Australia, lokacin da ya kai ziyara mujami'ar St Thomas' Anglican Church, inda ya bayyana jin dadinsa a fili game da tarbar da ya samu.

Karin bayani:Sarki Charles na Ingila na ziyara a Kenya

Wannan ita ce ziyarar sarkin ta farko a kasar waje, tun bayan da ya kamu da cutar kansa, kuma wannan ce ziyararsa ta 16 a kasar Australia, wadda ya yi karatu a cikinta lokacin yana matashi a shekarar 1966. 

Karin bayani:An nada Sarkin Ingila bayan shekaru 70

Haka zalika sarki Charles ya kai ziyara majalisar dokokin jihar New South Wales, wadda ke bikin cika shekaru dari biyu da kafuwa.

Bayan kammala ziyarar ta kwanaki 6 ne sarkin zai halarci taron kungiyar kasashen rainon Ingila ta Commonwealth, da za a gudanar a Samoa.