Sarki Abdallah a Jamus | Labarai | DW | 08.11.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Sarki Abdallah a Jamus

Sarki Abdullah na kasar Saudi Arabia zai fara rangadin aiki na kwanaki uku daga yau,anan tarayyar jamus.Ayayinda yake wannan kasa zai fara ganawa ne da shugabar gwamnati Angela Merkel,inda zasu tattauna shirin SAudiyya na daidaita dangantaka tsakanin Izraela da sauran kasashen Larabawa.A jiya a birnin Rome dai Sarki Andallah ya gana da Paparoma Benedict na 16,a wata ganawa da take zama na farkon irinsa tsakanin shugaban darikar Roman katholika da wani sarki na Saudiyya.Anasaran Sarki Abdallah,wanda tuni ya ziyarci kasashen britania da Switzerland,daga nan Jamus zai wuce kasar Turkiyya.